• Leadership Hausa
Thursday, September 28, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zulum Ya Ba Da Umarnin Bude Ofishin NNPP Da Aka Rufe A Borno

by Sadiq
1 year ago
in Siyasa
0
Zulum Ya Ba Da Umarnin Bude Ofishin NNPP Da Aka Rufe A Borno
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarni bude ofishin jam’iyyar NNPP da ke jihar ba tare da bata lokaci ba.

An ruwaito awaito cewa da yammacin Juma’a ne, gwamnan ya umarci Hukumar Raya Birane ta Jihar ta bude ofishin.

  • Martanin Wike Ga Lamido: Ba Ka Da Sauran Wata Kima A Siyasa
  • Anya, Guguwar Tsige Shugabannin Jam’iyya Ba Za Ta Ci Adamu Da Ayu Ba?

Hadimin gwamnan kan Kafafen Yada Labarai, Malam Isa Gusau, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da fitar a ranar Juma’a, inda ya ce bayan gwamnan ya samu labarin rufe ofishin ne ya bayar da umarnin sake bude shi.

Zulum, ya ce ko ma mene ne dalilin daukar matakin bai kamata a rufe ofishin a wannan lokaci ba.

Cikin sanarwar, Gusau, ya ce dama al’ummar jihar na da masaniya a kan cewa tun shekaru uku da suka wuce Hukumar Raya Birane jihar ke daukar matakan kawo gyara ciki har da rufewa wasu gine-gine na musamman wadanda ba a yi su bisa ka’ida ba.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke

Kotun Zabe Ta Ce Zaben Gwamnan Kaduna Bai Kammalu Ba (Inconclusive)

Hukumar ta ce ta dauki matakin rufe ofishin ne saboda rashin bin ka’idar da ta dace wajen bude ofishin.

Zulum, ya ce sake bude ofishin abu ne da kowa zai so sannan kuma yana da kyau a ba wa kowacce jam’iyya dama gudanar da ayyukanta ba tare da wata matsala ba.

A a ranar ne dai Alhamis ne hukumar ta rufe ofishin jam’iyyar wanda ke hade da wasu ofisoshinta.

Bayan rufe ofishin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah wadai da rufe ofishin jam’iyyar da aka yi.

A cikin wata sanarwa da Kwankwaso ya fitar a shafinsa a Twitter, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.

An rufe ofishin NNPP ne a yayin da Kwankwaso ke shirin zuwa jihar a karshen wannan makon.

Tags: BornoGusauHukumar Raya BiraneKwankwasoNNPPOfishiRufewaZulum
ShareTweetSendShare
Previous Post

Martanin Wike Ga Lamido: Ba Ka Da Sauran Wata Kima A Siyasa

Next Post

Matakan Samun Nasarar Kasuwanci Mai Dorewa

Related

Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke
Manyan Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke

5 hours ago
Kotun Zabe Ta Ce Zaben Gwamnan Kaduna Bai Kammalu Ba (Inconclusive)
Manyan Labarai

Kotun Zabe Ta Ce Zaben Gwamnan Kaduna Bai Kammalu Ba (Inconclusive)

7 hours ago
NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara
Siyasa

NNPP Ta Kai Korafinta Ga Hukumar NJC Kan Kalaman Daya Da Cikin Alkalan Kotun Zaben Kano

2 days ago
Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamna A Legas Za Ta Yanke Hukunci Ranar Litinin
Manyan Labarai

Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamna A Legas Za Ta Yanke Hukunci Ranar Litinin

5 days ago
Shari’ar Zaben Gwamnan Bauchi: Sai Mun Ga Abin Da Ya Ture Wa Buzu Nadi – Dan Takarar APC
Siyasa

Shari’ar Zaben Gwamnan Bauchi: Sai Mun Ga Abin Da Ya Ture Wa Buzu Nadi – Dan Takarar APC

6 days ago
NNPP Ta Maka Kwankwaso A Kotu Kan Zargin Yi Wa Jam’iyya Makarkashiya
Manyan Labarai

NNPP Na Zargin Kwankwaso Da Hannu Wajen Nasarar Gawuna Da Kwace Zaben Kano A Kotu

7 days ago
Next Post
Matakan Samun Nasarar Kasuwanci Mai Dorewa

Matakan Samun Nasarar Kasuwanci Mai Dorewa

LABARAI MASU NASABA

An Lakadawa Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya Duka A Kano

An Lakadawa Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya Duka A Kano

September 28, 2023
Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Ghana Na Da Muhimmanci Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Ghana

September 28, 2023
Bamu Da Niyyar Cin Zarafin Victor Osimhen-Napol

Bamu Da Niyyar Cin Zarafin Victor Osimhen-Napol

September 28, 2023
Adadin Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Kasashen Waje A Shekarar 2022 Na Kan Gaba A Duniya

Adadin Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Kasashen Waje A Shekarar 2022 Na Kan Gaba A Duniya

September 28, 2023
Cibiyar Kimiyyar Noma Na Sin CATAS Ta Cancanci Yabo

Cibiyar Kimiyyar Noma Na Sin CATAS Ta Cancanci Yabo

September 28, 2023
CISA: Masana’antun Sarrafa Karfe Na Tafiya Cikin Yanayi Mai Karko Tsakanin Watan Janairu Zuwa Na Agusta

CISA: Masana’antun Sarrafa Karfe Na Tafiya Cikin Yanayi Mai Karko Tsakanin Watan Janairu Zuwa Na Agusta

September 28, 2023
Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke

Gwamna Uba Sani Ya Taya Kansa Murna Da Hukuncin Da Kotun Zaben Kaduna Ta Yanke

September 28, 2023
Kungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango

Babu Wata Yarjejeniya Tsakaninmu Da Gwamnatin Tarayya Kan Dakatar Da Yajin Aiki – NLC

September 28, 2023
Masana Kimiyya Na Sin Da Afrika Sun Lashi Takobin Hada Gwiwa Wajen Ganin An Cimma Ajandar Kyautata Rayuwar Jama’a

Masana Kimiyya Na Sin Da Afrika Sun Lashi Takobin Hada Gwiwa Wajen Ganin An Cimma Ajandar Kyautata Rayuwar Jama’a

September 28, 2023
“Wasannin Asiya Na Zamani” Wata Taga Ce Ta Lura Da Yadda Ake Gudanar Da Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin

“Wasannin Asiya Na Zamani” Wata Taga Ce Ta Lura Da Yadda Ake Gudanar Da Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin

September 28, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.