• English
  • Business News
Saturday, October 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Banza Man Kare: Barazana Da Takunkumi Sun Daina Tasiri

by CGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
in Daga Birnin Sin
0
A Banza Man Kare: Barazana Da Takunkumi Sun Daina Tasiri
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

Yanzu shekarar ta 2025 muke ciki, kuma matakin da duniya ke daukawa wajen gudanar da al’amura ya bambanta da shekaru goma da suka gabata. Amma abin takaici shi ne, wasu har yanzu sun nace ma tsoffin dabaru, suna ganin barazanar haraji da takunkumi na iya mamaye duniya, na san kun riga kun san inda na dosa. Shugaban Amurka Donald Trump da aka rantsar a baya-bayan nan ya yi barazanar sanya harajin kashi 100 bisa 100 kan kasashen BRICS idan suka ci gaba da kokarin rage tasirin dala. “A matsayinsu na al’ummar BRICS, za a kakaba musu harajin kashi 100 bisa 100 idan har suna tunanin aiwatar da abin da suke tunani, don haka za su yi watsi da hakan nan take.” Wannan na daga cikin kalamansa a ranar farko da ya hau kan karagar mulki. Muna iya cewa wannan na daya daga cikin sumbatunsa da ya saba yi, saboda sanin kowa ne cewa, ba a kafa BRICS don ta yi jayayya, ko sa-in-sa da kowa ba, sai dai don karfafa hadin gwiwa da samun wadata, kuma gaskiyar magana ita ce, yanzu kasashen duniya sun daina tsoron mamayar kudin wata kasa ko matsin lamba na takunkumi.

Mu dauki Rasha a matayin misali, lokacin da ta fuskanci dimbin takunkumi daga kasashen yamma a 2014 da 2022, da yawa sun yi hasashen durkushewar tattalin arzikinta. Maimakon haka, Rasha ta samar wa kanta mafita ta hanyar tsarin hada-hadar kudi na cikin gida wato SPFS, wanda ba ya bukatar tsarin hada-hadar kudi na yammacin duniya, wannan yunkurin ya yi wa tattalin arzikin Rasha garkuwa tare da aza harsashi na zurfafa dangantakar hada-hadar kudi da kawayenta kamar Turkiya, Kazakhstan, har ma da al’ummomi a Gabas ta Tsakiya, tare da yin watsi da tsarin kasashen Yamma. Hakazalika, Amurka ta hana Turkiya damar amfani da fasaha da wasu kayayyakin aiki na Amurka, kama daga jiragen F-35 zuwa jiragen sama marasa matuka. Sakamakon haka shi ne, a halin yanzu Turkiya na kera wasu daga cikin wadannan kayayyakin aiki da albarkatunta har ma ta fara fitar da kayayyaki zuwa wasu kasashen Gabas ta Tsakiya da Afirka. Haka ma kasashen BRICS su ma sun yi ta sake fasalin ka’idojin cinikayyar duniya. Sun koma ga amfani da nasu kudade wajen gudanar da kasuwanci a tsakaninsu, suna rage dogaro da dalar Amurka. Hakazalika, Brazil da Sin na yin cinikayya da kudaden kasashensu, matakin da Indiya da kawayenta na yankin suke koyi da su. Yanzu dai kan mage ya waye, kuma kasashen duniya sun fahimci cewa hadin gwiwar samun moriyar juna tare da dunkulewar duniya waje guda su ne mafita ga kalubalen da duniya ke fuskanta, kuma wannan shi ne makasudin kafa BRICS. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Lokaci Ya Yi Da Za A Kawo Karshen Fashewar Tankar Mai A Nijeriya – Shettima

Next Post

Firaministan Sin Ya Tattauna Da Baki Kwararru Dake Kasar

Related

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa
Daga Birnin Sin

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

3 hours ago
Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

4 hours ago
Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

5 hours ago
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci
Daga Birnin Sin

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

6 hours ago
Xi Da Takwaransa Na Bangladesh Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Alakar Kasashensu
Daga Birnin Sin

Xi Da Takwaransa Na Bangladesh Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Alakar Kasashensu

8 hours ago
Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo
Daga Birnin Sin

Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

1 day ago
Next Post
Firaministan Sin Ya Tattauna Da Baki Kwararru Dake Kasar

Firaministan Sin Ya Tattauna Da Baki Kwararru Dake Kasar

LABARAI MASU NASABA

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

October 4, 2025
Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

October 4, 2025
Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

October 4, 2025
Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

October 4, 2025
Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.