Muna amfani da wannan dama muna baiwa abokin aikinmu na Freedom Radio Kano 99.5 FM, Malam Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, hakuri kan labarin da wakilinmu ya wallafa bisa kuskure ba tare da ya bin tsarinmu na tantance labari kafin a wallafa ba.
Dukda cewa wakilin namu ya ce, ya samu kuskuren fahimtar fuskantar labarin yadda ya dace bisa kuskuren cewa, Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano ya ce, “Ganduje ya sauka daga kujerarsa sannan Kwankwaso zai koma APC” Alhali ba haka ainihin labarin yake ba.
- Ni Ne Jagoranku Da Zarar Kun Dawo APC, Ganduje Ga Kwankwaso
- Ganduje Ya Zargi ‘Yan Siyasa Da Hannu A Haddasa Rikice-rikicen Zabe
Wannan labarin ba gaskiya ba ne, kuskure ne mai girma, kuma a hukumance za mu dauki matakin ladabtarwa kan wannan ma’aikacin namu don gudun sake maimaituwar irin wannan a nan gaba.
Muna ba da hakuri kan wannan kuskuren ga, Malam Dan’uwa Rano da abokan huldarmu da dumbin masu bibiyar shafukanmu na sada zumunta.
Mun gode
Daga: Shugaba mai kula da shafukan sadarwa na Sashen Hausa na Leadership.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp