Kwanan nan, bisa sulhun da kasar Sin ta yi, kasashen Saudiyya da Iran sun farfado da huldarsu bayan da suka katse huldar jakadanci na tsawon shekaru bakwai, lamarin da ya bude sabon babin dangantakar kasashen biyu, baya ga yadda hakan ya haskaka duniyarmu da ta shiga duhu sakamakon matsalar Ukraine.
Yadda Saudiyya da Iran suka farfado da huldarsu abu ne mai ma’ana ga kasashen biyu, baya ga haka, yana kuma da muhimmanci ga sauran kasashen duniya. Na farko, lamarin ya shaida mana cewa, kasa da kasa na iya zama lafiya da juna da tabbatar da cin moriyar juna bisa tushen martaba juna. Na biyu kuma, ya haifar da wani yanayi na rungumar zaman lafiya a shiyyoyin gabas ta tsakiya da arewacin nahiyar Afirka da suka dade suna fuskantar tashin hankali, har ma da duniya baki daya.
In mun waiwayi baya, za mu fahimci cewa, Amurka da sauran kasashen yamma ne suka yi ta tada rikici da jawo rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen gabas ta tsakiya da arewacin nahiyar Afirka, kuma kasancewar Saudiyya da Iran manyan kasashen shiyyar, sun tabka mummunan hasara sanadiyar hakan,har daga baya suka gane halin kasar Amurka tare da fahimtar cewa, ta hanyar yin shawarwari da juna ne kawai za su iya fita daga mawuyacin halin.
Matsalar Ukraine da aka shafe sama da shekara guda ana fama da ita, ita ta hannun Amurka, kuma har yanzu Amurka na kokarin rura wutar rikicin. A ranar 20 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa, kasarsa za ta kara samar da gudummawar soji da darajarta ta kai dalar Amurka miliyan 35 ga Ukraine. Alkaluma sun shaida cewa, ya zuwa tsakiyar watan Janairun bana, gaba daya Amurka ta samar da gudummawar soja da ta kai dala biliyan 46.6 ga kasar Ukraine, adadin da har ya wuce matsakaicin kudin da ta ware ga yakin Afghanistan a kowace shekara. Kwatankwacin abubuwan da Amurka ta aikata, a cikin shekara sama da daya tun bayan aukuwar rikicin Ukraine, kasar Sin ba ta taba tsayawa tana kallon rikicin ba, ballantana ta rura wutar rikicin, a maimakon haka kuma, ta yi ta kokarin gano bakin zaren warware shi. Idan ba mu manta ba, a ranar 24 ga watan Faburairun da ya wuce, kasar Sin ta fitar da takardar da ke bayani kan matsayinta a kan warware matsalar Ukraine a siyasance, inda ta samar da dabararta a wani kokari na daidaita matsalar a siyasance.
A hakika irin bambancin matakan da kasashen Sin da Amurka suka dauka ya faru ne sakamakon bambancin da suka samu ta fannin fahimtar tsaron kasa da kuma cudanyar kasa da kasa. Misali a game da tsaron kasar, kasar Sin na dora muhimmanci a kan tsaron kanta da ma na sauran kasashen duniya baki daya, don gina al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya, a yayin da Amurka ke nuna son kai wajen kiyaye tsaron kanta, kuma tana daukar barazanar da moriyarta ke fuskanta a kowane bangaren duniya a matsayin abin da zai illata tsaronta. A game da cudanyar kasa da kasa kuma, manufar kasar Sin ita ce zama lafiya da juna tare da martaba bambancin juna ta fannoni daban daban, a yayin da Amurka ke ganin duk wadda ke da bambancin ra’ayi da ita ba za ta taba zama abokiyarta ba, sai ma ta zama abokiyar gabanta.
Kasancewarsu a duniya guda, makomar dan Adam ma daya ce. A cikin ‘yan shekarun baya, kasar Sin ta gabatar da shawarar raya duniya da shawarar kiyaye tsaron duniya da ma shawarar raya wayewar kan duniya, a wani kokari na tabbatar da dauwamammen zaman lafiya a duniya, ta yadda kowace kasa za ta kasance cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma kowace kasa za ta samu hakkin tabbatar da ci gabanta, kuma al’ummar kasa da kasa za su ji dadin zaman rayuwarsu. A ganina, wannan shawarar da kasar Sin ta gabatar, ta kuma kasance buri na bai daya na al’ummar duniya.(Mai Zane:Mustapha Bulama)