• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Karon Farko Iyayena Ba Su Amince Da Shigata Fim Ba —Fatima Moh’d

by Rabi'at Sidi Bala
2 years ago
in Nishadi
0
A Karon Farko Iyayena Ba Su Amince Da Shigata Fim Ba —Fatima Moh’d
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Fitacciyar Jarumar cikin shiri me dogon zango na Kwana Casa’in, Fatima Moh’d wadda aka fi sani da AMINA MATAR SAMBO, Ta bayyana irin kalubalen da ta rinka fuskanta wajen mutane dangane da shirin kwana casa’in, inda ta yi bayani game da irin mastalolin da ta fuskanta kafin shigarta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Jarumar da ta shafe shekaru goma a cikin masana’antar ta yi kira ga gwamnati tare da jan hankalin masu kokarin shiga harkar fim, har ma da na cikin masana’antar. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka;

  • ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
  • Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki.

Sunana Fatima Mohd Gwammaja, wadda aka fi kira da Amina Matar Sambo. An haife ni a Unguwar Gwammaja, karamar hukumar Dala. Na yi karatun ‘Primary, Secondary, N.C.E’, duk a garin Kano, sai kuma a yanzu gani ina gwagwarmaya a masana’antar kannywood ana neman na abinci, sai kuma ‘Teaching’ da nake yi a Sakandare.

Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin masana’antar Kannywood?

Labarai Masu Nasaba

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

Abubuwa da yawa. Ina sha’awar na ga ina bada gudumawa ta hanyar isar da sako a finafinan wasan kwaikwayo.

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?

Kamar yadda na ce miki ni ‘yar Gwammaja ce, kuma gidan mu yana kusa da ofis din ‘SARAUNIYA FILM PRODUCTION’, kin ga zan sami gudumawa ta hanyar san shiga da sanin jaruman da zan sami tsanin shiga. Kuma na sami tsanin shiga ta hanyar Jarumi Ali Rabiu Ali (Daddy).

Ya batun iyaye fa, lokacin da za ki sanar musu kina son shiga harkar fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su?

Gaskiya an sha gwagwarmaya, domin sam! iyayena ba su amince ba, na so harkar fim tun ina firamare amma sam sai suka ki, suka maida hankalina a kan karatu, amma da Allah ya sa ina da rabo a ciki gashi yanzu muna yi kuma da yaddar su. Mafi yawan Jarumai in za su shiga zai wuya  iyaye su yadda, musamman mu ‘yan Kano ba sa so, amma yanzu gashi ana ciki har da saka albarkar su.

Za ki kamar shekara nawa a cikin masana’antar Kannywood

Zan yi kamar shekara goma.

Kin yi fina-finai sun kai kamar guda nawa?

Ina da fina-finai da yawa, Ina da fim sama da dari biyar 500.

A wanne fim kika fara fitowa?

Fim din ‘Yarda’, na fito ni da Jarumi Mustapha Musty.

Wanne rawa kika taka cikin fim din, kuma ya farkon farawarki ya kasance, musamman yadda ya ke shi ne farkon farawarki a lokacin?

Ni ce Jarumar fim din, kuma na samu kaina a wani yanayi na daban, da ya shafi farin ciki, mamaki, da kuma samun nutsuwar samun ra’ayin zubiyata.

Ya karbuwar fim din ya kasance a wancen lokacin?

Ya karbu sosai, saboda lokacin ana siyan CD ne, sabanin yanzu da muka koma Youtube.

A gaba daya fina-finan da kika fito, wanne ne ya zamo bakandamiyarki?

Bakandamiyata fim 4 ne, Kwana casa’in, Ni da Mijin Yayata, Dabi’ar Zuciya, Hudubar Uwa.

Bayan kwana Casa’in da kika fito ciki, ko akwai wasu fina-finan masu dogon zango da kika fito ciki?

Ina da fim mai dogon zango sama da hamsin 50, kamar; Ni da Mijin Yayata, Madubi, Dabi’ar Zuciya, Halin So, Hudubar Uwa, Kudin Gado, Mene ne Sila, Zahiri Ko Badini,  Salon Damfara, Rayuwa Da Tarko, da dai sauransu.

Me kike son cimma game da fim?

Duk abin da nake so na cimma na samu sai fatan rayuwa tai karko, a yi fatan kar a yi karkon kifi a yi fatan karkon Dabino.

Wanne irin nasarori kika samu game da fim?

Abubuwan da ake mallaka na more rayuwa, dai dai gwargwado an samu, sai fatan Allah ya karo su, Hausawa suna cewa a sanka a san cinikinka, to Alhamdulillah an sanni a duniya wannan shi ne babban abun alfaharina.

Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta game da fim?

Dukkanin abin da ke da nasara baya rasa  kalubale a rayuwa, da yawa mutane suna ganin ka ki Aure saboda fim, wasu ma ‘direct’ suke fada Aure ya fi wannan sana’ar, sai kuma a fim din Kwana Casa’in a kashi na 5 sai da na koma rufe fuskata, saboda zagi da mutane ke yi a kan na ci amanar mijina Sambo, hakika ban ji dadi ba da ni da iyayena a wannan lokacin.

Bayan da hakan ya faru kin yi kokarin barin shirin, ko kuma sanar da masu shirin halin da kike ciki game da yadda sauran al’umma ke miki mummunan kallo ta yadda labarin ya zo, ko kuwa a haka kika ci gaba da yi?

Hahaha an kira ni a ‘program’ din ‘Gari Ya Waye’, na bawa mutane  hakuri na fahimtar da su dalilin haka.

Daga lokacin kika daina fuskantar kalubalen kenan?

Ai matsala ba za ta kare ba a rayuwa, sai dai a sami saukin, wani abun idanuwan jama’a a fuskar Jarumai take sai dai mutum ya yi kaffa – kaffa da kansa.

Kamar yadda kuke fuskantar matsaloli makamancin hakan, ta yadda labari ke zuwa na kwarai ko akasin hakan, shin ku kan yi kokarin zabar irin rawar da za ku taka  cikin fim wani lokacin, ko kuwa dole iya wanda aka zaba maka shi za ka yi?

Ai ko wane Jarumi da irin basirar sa, kuma su masu shirya fim suna sanin irin rawar da muke takawa, dan haka idan suka zabi mutum suna kiransa ya zo Odition domin tabbatar da zai iya. Ina cikin Jarumar da nake yin ko wane ‘roll’ dan haka Ina yin ko wane iri.

A cikin shirin kwana casa’in, wanne waje ne ya fi birge ki, kuma wanne waje ne ya fi baki wahala?

Abin burgewa a gare ni  shi ne; a zaman kotu da ake tuhumar Sambo laififfikansa na kashe-kashe da ya yi, domin ya amsa laifinsa ne, idanunsa na kaina wannan ya jawo hankalina ya tashi har na kasa fita a kotu wannan guri ya dauki hankalina kuma ya burge ni.

Me za ki ce da masu kallon, game da irin kallon da suke yi muku na daban, musamman na rashin yin aure, da kuma wajen taka rawa na yadda labarin ya zo da shi wanda ba na kwarai ba?

Ina kira ga ‘yan kallo da su rinka yi mana uzuri, shi fa abin da muke aikatawa a fim kamanceceniya ce na halayyar wani ko wata ake samu mu yi, domin wayar da kan jama’a akan su nisanci wannan halin, ba fa shi ne halinmu na ainahi ba. Dole sai mun nuna wa mutum fadakarwa ta hanyar isar da sako da  wasa har mutum ya gane wannan halin. Batun aure kuma hakika muna fatan yin Aure idan suka ga ba mu yi ba, lokaci ne bai yi ba, sai mu yi fatan nesa ta zo kusa.

Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin hakan, wanda ba za ki taba iya mantawa da shi a rayuwarki ba?

Farin cikina da ba zan. Manta ba bai wuce soyayyar masu kallo da muke samu ba. Kuma ba ni da wani abin bakin ciki da ya taba samu na wanda har zan saka shi a raina.

Ya kika dauki fim a wajenki?

Sana’a mai mahimmanci wacce take rike da ni, kuma ta gina ni.

Da wanne Jarumi ko Jaruma kika fi so a hada ki fim da shi/ita?

Bani da zabi kowanne Jarumi aka bani kawai a fara aiki, kowa nawa ne a jarumai.

Wanne fim ne idan kika tuna kike da kin sanin yinsa?

Babu gaskiya sam! ban da shi.

Shin kin taba aure ko tukunna dai?

A’a! Ban taba aure ba.

Toh ya batun soyayya a kannywood, ko akwai wanda ya taba cewa yana sonk har ta kai da kun fara soyayya tare cikin masana’antar?

Mun fi yin soyayya a waje gaskiya, gaskiya babu.

Kamar wanne lokaci kike sa ran yin aure, tunda Aure lokaci ne?

Ko yanzu ya zo na shirya.

Wanne irin namiji kike son aura?

Ba ni da zabi sai na Allah.

Da yawan mutane na yi wa jaruman fim mummunan kallo hadi da yi musu kudin goro na rashin tarbiyya da aikata badala, me za ki ce akan hakan?

A rinka yi mana duba na adalci da mutunci, a rinka yi mana duba mai kyau kar a rinka aibata mu.

Wanne irin kallo sauran ‘yan unguwa, ko ‘yan uwa da kawaye suke yi miki, musamman idan za ki fita zuwa wani waje naki daban, ko kuma idan kin shiga cikinsu?

A gaskiya a baya an sanar da ni zan shiga harka mara kyau, amma yanzu fatan alkhairi ake min.

Mene ne burinki na gaba game da fim?

Burina ko bayan raina na ga ci gaban Kannywood.

Wanne kira za ki yi ga masu kokarin shiga harkar fim?

Ina Kira ga duk wanda ke sha’awar shiga kofa a bude take matukar zai bi dokokin masana’anta, iyaye su zo su saka maka hannu da kansu.

Me za ki ce ga sauran abokan aikinki?

Ina kira da mu zama tsintsiya madaurinki daya a gudu tare a tsira tare.

Me za ki ce da makaranta shafin Rumbun Nishadi?

Ina yi musu fatan alkhairi, su ci gaba da kasancewa tare da wannan shafin, ba su kadai ba har ni ma zan ci gaba da kasancewa tare da shafin Rumbun Nishadi.

Me za ki ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?

Ina godiya a gare su tare da fatan Allah ya kara musu daukaka.

 

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ali Rabiu Ali, Sani Ahmad Kankarofi, Usman Adam.

Muna godiya ki huta lafiya

Ni ma na gode.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Fati MuhdJarumaKannywoowdKwana Casa'inSambo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Dubi Ga Amfanin Jajircewa A Gwagwarmayar Siyasa

Next Post

Maraba Da Azumin Ramadan Na Bana

Related

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro
Nishadi

Har Yanzu Da Bazar Mahaifina Nake Rawa -Hanafi Ibro

4 days ago
Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage
Nishadi

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

4 days ago
Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe
Nishadi

Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe

2 weeks ago
Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
Nishadi

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje

3 weeks ago
Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda
Nishadi

Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda

3 weeks ago
Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri
Manyan Labarai

Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri

3 weeks ago
Next Post
Maraba Da Azumin Ramadan Na Bana

Maraba Da Azumin Ramadan Na Bana

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

May 15, 2025
Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa

Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa

May 15, 2025
An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

May 15, 2025
NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC

NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC

May 15, 2025
Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu

Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu

May 15, 2025
Lassa Da Shawara Sun Kashe Mutum 183 A Jihohi 36 Da Abuja

Lassa: Mutane 138 Sun Rasu, 717 Sun Kamu A Jihohi 18 – NCDC

May 15, 2025
Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda

May 15, 2025
ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

May 15, 2025
‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

May 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.