Harkokin karatu da karantarwa da ma jarabawar ɗalibai sun tsaya cak a Jami’ar Sakkwato, bayan da ƙungiyar Malaman Jami’ar suka tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba 26 ga watan Fabrairun 2025.
Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyar malaman suka fara yajin aiki tun bayan kafuwar jami’ar sama da shekaru 12 da suka gabata.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Tabbatar Da Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Duba Ƙarin Farashin Wutar Lantarki
Cikin sanarwar da shugabansu, Saidu Isah Abubakar, tare da Sakataren Jami’ar, Hassan Aliyu, suka fitar, sun bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne domin tilasta wa gwamnatin jihar biyan buƙatun da suka jima suna gabatarwa.
Kazalika sun yi ƙorafi tare da nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnati da majalisar gudanarwar Jami’ar ke tafiyar da al’amuran da suka shafi ci gabanta.
Ƙungiyar malaman ta ce ta kafa wani kwamiti da zai tilasta tare da tabbatar da an bi umarnin yajin aikin da tsayawar harkoki a Jami’ar har sai an cimma matsaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp