Matsalar tsaro a Nijeriya na kara ta’azzara inda a karon farko a ranar Talata, ‘yan bindiga suka kai harin kwanton bauna ga tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke hanyarta ta zuwa garin Daura don shirye-shiryen tarbar shugaban da kuma tsara hidindimun sallah da shugaban zai yi a can.
A cikin ayarin motocin akwai jami’an tsaro da hakimai da ‘yan jarida na fadar shugaban kasa wadanda aka farmake su a Dutsinma da ke Jihar Katsina.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa mutum biyu sun samu raunika lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa ayarin motocin shugaban kasa kwantan-bouna.
Lamarin ya faru ne gabanin zuwan Shugaba Buhari garin Daura domin gudanar da bikin babbar sallah a mahaifarsa a ranar Asabar.
An dai rawaito cewa wannan harin na tawagar motocin shugaban kasa ya afku ne jim kadan bayan kashe Mataimakin Kwamishinan ‘Yansandar na Dutsinma a wani lamari na daban.
Wani ganau ya bayyana wa manema labarai cewa tawagar motocin tana kan hanyarta ce ta zuwa Dutsinma daga Kankara, inda ta ci karo da daruruwan ‘yan bindiga kan babura sun tsare hanya, daga nan tawagar ta watse tare da gudun ceton rai.
An ce maharan sun ci karfin jami’an tsaro da ke cikin ayarin motocin shugaban kasan, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.
“Muna cikin tafiya sai muka ga ‘yan bindiga a kan babura sun datse hanya. Mun yi kokarin gudu zuwa kauyen Turare, nan take sojoji suka kawo dauki tare da tarwatsa ‘yan bindigan.
“Bayan musayar wuta a tsakani, sojoji sun sami nasarar share hanya wanda a nan ne muka sami damar shiga garin Dutsinma,” in ji shaidun gani da ido.
Wani wanda lamarin ya kusa rutsawa da shi a kauyen Turare ya bayyana cewa bayan sojoji sun tabbatar da fatattakar ‘yan bindigar, gungun ‘yan bindigan ya kara kai farmaki wasu kauyukan a gundumar Makera da ke cikin karamar hukumar Dutsinma da kuma wasu kauyuka a yammacin Zobe Dam, inda suka yi awon gaba da shanu masu yawa.
“Sun shiga yankunan Makera, Kurechi, Dogon ruwa, Tashan Mangwaro da sauran wasu kauyuka, inda a nan ne suka yi awon gaba da shanu masu yawan gaske.
“Har zuwa yanzu da nake magana, wasu daga cikin mazauna wadannan kauyuka sun yi gudun hijira zuwa garin Turare saboda tsoron sake kawo musu hari,” in ji shi.
Mashawarcin shugaban kasa ta fannin yada labarai, Garba Shehu, ya tabbatar da farmakin tawagar ayarin motocin shugaban kasan, ya bayyana cewa mutum biyu sun samu rauni.
“Fadar shugaban kasa tana bayyana wannan lamari a matsayin abun takaici na kai wa tawagar motocin shugaban kasa hari kusa da Dutsinma da ke Jihar Katsina, wanda daga ciki akwai jami’an tsaro da hakimai da ‘yan jarida wadanda za su tarbi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari idan ya isa garin Daura domin gudanar da bukukuwan babbar Sallah.
“Maharan sun bude wuta a kan ayarin tawagar motocin shugaban kasa lokacin da suka yi musu kwantar-bauna, sai dai sun samu dauki daga wurin sojoji da ‘yansanda, da jami’an tsoro na farin kaya (DSS).
“Mutum biyun da suka samu raunika daga wannan hari suna amsar magani a asibiti. Dukkan sauran jami’an da motocin suna cikin koshin lafiya a garin Daura,” in ji shi.
Bayan farmakin da ‘yan awanni kuma wasu ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne dauke da muggan makamai da bama-bamai suka kai hari a gidan yarin Kuje da ke Abuja tare da kashe mutane biyar da jikkata da dama.
Bayanai sun nuna mutum biyar suka rasa ransu tare da raunuka da wasu 19 suka samu a wannan harin.
Harin ya tada hankalin fursunonin da suke tsare a gidan yarin a wannan lokacin tare da arcewa da wasu fursunoni da masu tsaron gidan yarin suka yi domin tsira da rayukansu daga harin da ‘yan ta’addan suka kaddamar.
Wakilinmu ya tattaro cewa, maharan sun kwashe tsawon awa guda suna cin karensu babu babbaka kafin daga bisani suka kammala abun da suka je yi gami da yin gaba.
Kasa da awanni 24 da faruwar lamarin, gwamnatin tarayya ta fito ta ce ana zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai harin domin kubutar da mambobinsu da suke tsare a wannan gidan yarin.
Wasu fursunoni a daidai lokacin da harin ke aukuwa, sun shaida wa ‘yan jarida cewa lamarin ya kazanta kuma lallai babu wanda hankalinsa bai tashi a cikin gidan yarin ba, sun ce, fursunonin da suka gudu da dama sun yi hakan ne domin tsira da rayukansu.
Suka ce: “Muna nan dai kawai muka fara jin ana ta harbo ‘roket-roket’ jami’an gidan yarin kuma suna ta fita. An fara wannan harbe-harben ne wajen karfe goma na daren ranar Talata kuma sun shafe tsawon mintina arba’in suna ta harbe-harbensu. Sun yi ta harbo roket din ne daga babbar mashigar gidan yarin ta baya.”
Sun kara da cewa, a lokacin da aka kawo musu harin akwai sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da dama amma duk maharan sun tarwatsa su, “Ana ta tunanin wadanda suka kawo wannan hare-haren ‘yan Boko Haram ne, amma da yake mu muna cikin gidan yarin a tsare ba mu iya ganinsu da idonmu ba.
“Dukkanin ma’aikatan da ke kula da mu sun gudu, wasu fursunoni da dama su ma sun tsere.”
Sun ce, a lokacin da ake ta harbe-harben nan kowa neman inda zai gudu kawai yake, “Hatta mu da muke wannan maganar neman hanyar guduwa muke.”
Sun tabbatar da cewa, masu kai harin sun fi matsa kaimi ta inda ake tsare da wasu mambobin Boko Haram a cikin gidan yarin.
A harin da aka kai din, fursunoni 879 ne suka tsere daga gidan yarin na Kuje, inda hukumomi suka tabbatar da cewa sun samu nasarar sake kamo fursunoni 551 daga cikin wadanda suke gudun, a lokacin da ake rubuta wannan rahoton. Har ila yau zuwa ranar Laraba da yamma, fursunoni 328 ne suka gudu ba tare da an iya gano inda suke ba tun bayan harin da aka kai din.
Sai dai kuma, daya daga cikin jami’an hukumar tsaro ta fararen hula (NSCDC) da ke aiki a gidan yarin ya riga mu gidan gaskiya sakamakon harin yayin da wasu jami’an tsaro su uku suka gamu da munanan raunuka.
Hukumar kula da gidajen yarin Nijeriya NCoS, ta kuma tabbatar da cewa, wasu fursunoni hudu su ma sun mutu sakamakon harin tare kuma da wasu fursunoni 16 da suka samu manyan raunuka daban-daban.
Jami’in watsa labarai na gidan yarin Nijeriya, AD Umar, ya bayyana cewar lamura sun dawo daidai bayan harin, “Jami’an tsaron gidan yarin da sauran jami’an tsaro sun yi kokarin maida martani wajen kwato ragamar gidan yarin kuma zuwa yanzu lamura sun daidaita.”
A sanarwar manema labarai da Umar Abubakar, ya fitar, ya bayyana cewar “Maharan sun kawo hari dauke da manyan abubuwan fashewa inda suka kutsa kai ta babbar mashigar gidan yarin.
Jami’in NSCDC daya da wasu fursunoni hudu sun mutu. Muna kuma kan kokarin kamo sauran fursunonin da suka tsere.”
“Muna kuma tabbatar wa jama’a cewa, DCP Abba Kyari da sauran manyan mutanen da ke tsare a gidan yarin ba su tsere ba. Har yanzu suna cikin gidan yarin.”
Ya ce, za su yi amfani da sabbin hanyoyin zamani wajen ganin sun kamo wadanda tseren tare kuma da cewa, zuwa yanzu an sake karo adadin jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a gidan yarin.
Ya kuma ce, wasu daga cikin masu kawo harin su ma an kashe wasu daga cikinsu kuma wasu da dama sun gudu da raunuka.
Ya ce, Kwantirola Janar na gidan yarin Nijeriya, Haliru Nababa ya jinjina wa irin kokarin da jami’an tsaro suka nuna tare da irin gudunmawar da suka ba su, ya bukaci jama’an Nijeriya da suke taimaka musu da bayanai a kowani lokaci domin kiyaye gidan yarin da ke kasar nan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yada zango a gidan yarin Kuje a kan hanyarsa ta zuwa kasar Senigal inda ya nuna rashin jin dadinsa da harin.
Shugaban kasan wanda ya je gidan yarin Kuje da yammacin ranar Laraba a lokacin da ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgi ya gane wa idonsa irin barnar da ‘yan ta’addan suka yi a gidan yarin na Kuje.
A bangaren gwamnatin tarayya kuwa, Babban sakataren ma’aikatar kula da harkokin cikin gida a Nijeriya, Mista Shuaibu Belgore, a ranar Laraba da ya ziyarci gidan yarin da abun ya faru, ya ce, gwamnati ta yi tir da harin kuma za a tabbatar an dakile faruwar makamancin hakan a nan gaba, ya ce wadanda suka tsere daga gidan yarin za a yi kokarin kamo su.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito, wannan harin na ranar Talata dai ba shi ne karo na farko da ‘yan ta’adda ke kai hari gidan yari a fadin kasar nan ba. Tare da kashe jami’an da suka tarar a bakin aiki.
Dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi tir da harin tare da cewa, rashin zartar da hukunci kan masu laifin da aka kama da laifuka ne ke kara baiwa ‘yan ta’adda sararin aikata danyen ayyukansu a Nijeriya.
Atiku wanda ke nuna takaicinsa kan harin gidan yarin Kuje, ya nuna matukar damuwarsa bisa yadda ta’addanci da aikace-aikacen ‘yan ta’adda ke kara kamari a kasar nan.
Ya ce, rashin zartar da doka da oda na cafkewa da zartar da hukunci kan wadanda aka kama da laifi na daga cikin dalilan da ke kara bai wa ‘yan ta’adda sararin aikata danyen ayyukansu.
Ita ma dai a martaninta kan harin na Kuje, jam’iyyar African Action Congress, ta ce, ‘yan Nijeriya na bukatar daukan matakin gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro da ya zama rowan dare a cikin kasar nan.
Jami’in watsa labarai na jam’iyyar, Adeyeye Olorunfemi, shine ya shaida hakan ta cikin sanarwar day a fitar a ranar Laraba, jam’iyyar ta yi Allawadai da wannan harin da aka kai gidan wa tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gidan yarin Kuje dukka a rana guda.
Ministan tsaron Nijeriya, Bashir Magashi, ya dora alhakin harin Kuje ga ‘yan Boko Haram, yana mai cewa akwai ‘yan boko haram sama da 64 a gidan yarin lokacin da harin ya wakana.