A wannan mako, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da dakatar da gudummawar da take samarwa Ukraine ta fannonin soja da ma leken asiri, biyowa bayan fadan da shugabannin kasashen biyu suka yi a ranar 28 ga watan da ya gabata a fadar White House, inda da ma suka yi shirin daddale yarjejeniyar ma’adinai. Sakamakon fadan, shugaban Ukraine ya bar White House ba tare da rattaba hannu a kan yarjejeniyar ba, don haka Amurka ta dakatar da gudummawar soja da ta leken asiri da take ba kasar Ukraine.
Lallai tsawon shekaru uku bayan aukuwar yaki a tsakanin Ukraine da Rasha, sabuwar gwamnatin Amurka ta zamanto “mai son wanzar da zaman lafiya” a tsakanin kasashen biyu daga wadda ta yi ta rura wutar rikicin tun farko. Har ma ta fake da sunan “Wanzar da dadadden zaman lafiya”, don bukatar Ukraine ta daddale yarjejeniyar ma’adinai da ita. Bisa ga yarjejeniyar, sassan biyu za su kafa wani asusu, wanda Amurka ke bukatar Ukraine ta zuba rabin kudaden da ta samu daga albarkatun ma’adinai na kasar cikinsa, har ma take yunkurin sa hannunta cikin ababen samar da mai da iskar gas na kasar. Akwai wani sharhin wata kafar yada labarai dake cewa, a zahiri hakan ya kasance yarjejeniyar mulkin mallaka ta fannin tattalin arziki a cikin karni na 21. Ai ba sabo da zaman lafiya sabuwar gwamnatin Amurka ke neman kawo karshen matsalar Ukraine ba, a’a, abin da take so shi ne ta ci karin moriya ta fannin tattalin arziki, kuma ta saba da yin hakan don cimma manufarta ta wai “Ba Amurka fifiko”.
- Za Mu Bai Wa Maraɗa Kunya A Wasanmu Da Manchester United – Arteta
- Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku
Mujallar The Economist ta wallafa wata mukala a shafinta a kwanakin baya cewa, shugaba Donald Trump ya fara neman iko a kasashen duniya ta hanyar nuna fin karfi da danniya, wanda hakan ya bayyana a fili a kasar Ukraine. Mukalar ta kuma yi nuni da cewa, yadda nuna fin karfi ya kasance tamkar “mai adalci” kuma ake cin zalin kasashe marasa karfi, na kara tabbata a duniyarmu.
Amma da gaske ne hakan zai tabbata? Ban yarda ba.
A gun taron wanzar da zaman lafiya da aka kira a birnin Paris sama da shekaru dari da suka wuce, Sinawa sun taba tambayar ko, “adalci ne zai ci galaba a kan fin karfi”, ko kuma “nuna fin karfi ne zai ci nasara a kan adalci?” A game da wannan, ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya ba da taikamaimiyar amsa a taron manema labarai da aka kira game da harkokin diplomasiyya a kwanakin baya, a gefen taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar da ke gudana a birnin Beijing, inda ya ce, bai kamata a mayar da hannun agogo baya ba. Kamata ya yi manyan kasashe su dauki nauyin da duniya ta dora a wuyansu, a maimakon su mai da hankali kawai a kan moriyarsu ko kuma su yi wa kasashe marasa karfi danniya.
Abin haka yake, akwai kasashe sama da 190 a duniyarmu, idan kowace kasa na bin manufar ba kanta fifiko, to nuna fin karfi zai zama a ko ina a duniyarmu, kuma kasashe masu karamin karfi su ne za su fi fuskantar matsalar. Amma abin farin ciki shi ne, har yanzu akasarin kasashen duniyarmu na rungumar adalci da zaman daidaito, kuma karin kasashe na rungumar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. A sa’i daya kuma, kasashe masu tasowa na kara karfinsu, inda suka riga suka zama muhimmin karfin da ke kiyaye zaman lafiya da sa kaimin ci gaban duniya.
Mutanen kasashen yamma su kan ce, “Moriya ta fi zumunta muhimmanci da dorewa”. Amma a ganin Sinawa, ya kamata abota ta dore har abada, kuma hakan zai tabbatar da moriyar kowa. Kamar dai yadda ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada, “Tarihi zai shaida cewa, wadanda suke rungumar kowa, su ne za su ci nasara. Hada kan juna don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, zai mai da duniyarmu ta zama ta kasa da kasa, tare da tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga kowa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp