• English
  • Business News
Wednesday, May 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Nijeriya Idan Ka Ce Za Ka Rike Aikin Gwamnati Shi Kadai Akwai Kalubale – Fatima (Adon Gari)

by Rabi'at Sidi Bala
3 years ago
in Ado Da Kwalliya
0
A Nijeriya Idan Ka Ce Za Ka Rike Aikin Gwamnati Shi Kadai Akwai Kalubale – Fatima (Adon Gari)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sana’a sa’a! in ji masu iya magana, yayin da wasu ke kallon kananan sana’o’i a matsayin sana’ar da ba ta dace da su ba, ko su rinka kallon wata sana’ar a matsayin sana’ar Maza kadai ba ta Mata ba, ko su Mazan su kalli sana’ar a matsayin ta Mata kadai ba ta Maza ba.

Sai ga shi sam! ba haka abin yake ba a yanuzu, domin akan samu Jajirtattun Mata wajen zakulo sana’a komai kankantarta dan guje wa zaman banza.

  • Ra’ayoyinku A Kan Labarin Budurwa Da Ta Gudu Da Motar Saurayinta Bayan Ya Je Sawo Mata Shawarma A Kano

Shafin Adon Gari ya zanta da wata jajirtacciyar matashiya mai sana’ar Kwalliyar Wurin Taro da ake ce wa ‘Dakwareshan’, wadda ta maida hankalinta ga sana’ar ta, FATIMA MUHAMMAD GHALI ta bayyana wa masu karatu irin gwagwarmayar da ta fuskanta kafin fara sana’ar ta har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’ar da kuma shawara ga masu aikin gwammnati a kab sy hada da sana’a. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:

Fatima
Fatima

Ya sunan Malamar?
Sunana Fatima Muhammad Ghali amma an fi sanina Ghali, a gida kuma Mummy ake ce min.

Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Eh! toh, ni dai an haife ni a garin Bauchi, na yi makarantar firamare da sekandare dina a ‘Special School Jibril Aminu Model Primary/Secondary School. Sannan na karanci ‘Human Anatomy’ a ‘Ahmadu Bello Unibersity Zaria’. Ba ni da aure, shekara ta ashirin da biyu.

Labarai Masu Nasaba

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata

Abin Da Ya Dace Ki Yi Yayin Haila Da Bayan Kin Gama?

Yanzu kina aiki ne ko ci gaba da karatu kike ko wata sana’ar?
Yanzu haka ina bautar kasa, Sana’a ta kuma ‘Decoration (kwalliya)’ ne, irin na suna, ‘bridal shower (bikin amare)’, ‘Birthday party (bikin zagayowar ranar haihuwa)’, ‘Henna party (bikin sa lalle)’, ‘Annibersaries (bikin cika shekara na wani abu)’, ‘Reunion (taron sake hada fuskoki)’, ‘family get-together (taron zumuncin iyali)’ da dai sauransu.

Me ya ja hankalinki har kika karkata ga wannan sana’ar?
Eh! toh, gaskiya na dade ina son abin da ya shafi ‘Decoration’, to bayan na gama makaranta na sai na fara. Sannan kuma a Nijeriya idan ka ce za ka rike aikin gwamnati shi kadai akwai kalubale, idan kana son ka ga albarkar aikin to ka yi Sana’a.

Za ki yi kamar shekara nawa kina yin ita wannan sana’ar?

Fatima
Ban kai shekara ba gaskiya, saboda sai bayan na gama makaranta ne na fara.

Farkon da za ki fara sana’ar, kin koya ne ko kin nemi shawarar wani ko wata game da yadda ake yi, ko kuwa da kanki kawai kika fara kokarin fara wa?
Sosai na nemi shawarwari, ‘in fact’ makarantar koyarwar da ‘Decoration’ din na shiga, ‘Kingebents’ shi ne inda na koya.

 

Ya za ki yi wa masu karatu bayanin yadda gwagwarmayar karatun ya kasance a takaice?
‘At first’ dai shiga makarantar ya dan yi wahala, duba ga masu ‘decoration’ ba su da yawa a garin Bauchi, na tuntubi gurare har uku amma da ke kullum suna cikin aikin ‘decoration’ na bukukuwa tun ina ‘300 level’ Kenan fa, ban samu ba, sai daga baya wanda na fara nema da farko wato ‘Kingebents’ na koma gurinsa bayan na yi ‘graduating’ kenan.

Kalubale dai tun kan ma a shiga aka fara fuskanta. Na yi wata uku ina zuwa kullum ban da Alhamis da Juma’a, toh shi ma hutun kwana biyun ‘assignment’ ake ba mu mu yi a gida kan abubuwan da aka koya mana. Za a baki ‘time’ in da za ki dau aikin a hoto ki tura idan kika wuce ‘time’ in za ki sha hukunci.

Aikin da farko dai bai ban wahala ba tun da kin san in kana son abu, wahalar dai kawai shi ne zuwa siyayyar kayan aiki ko da yaushe da kuma lokaci da muke dauka sosai farkon farawa, kamar ‘pumping’ iska a ‘balloon’ ya bani wahala saboda ciwon hannu sai na gwammaci na yi ta hurawa ‘balloon’ din da baki to shi ma idan na dawo ina shan fama da ciwon baki. Misali za a sa in hura ‘balloon’ guda dari, ina hurawa wasu na fashewa haka wajen nadawa, wasu su fashe dole in sake hura wasu kafin in gama dai zan dauki lokaci sosai.

Yawwa sai kuma idan ka gama aikin naka ‘for 3 hours’ bayan ka gaji fa sai a sa ka maida komai yadda yake da, ma’ana ka tattare kayan aikin to shi ma yana ba ni wahala lokacin. A hankali dai muka saba da yake ke shi ogan namu ya iya aikin sosai a hankali duk ya bi jikinmu. ‘Balloon garland’ na fara koya sai ‘Backdrop’ sai ‘clouding’, sai ‘traditional settings’ irin na su ‘Henna party’ da sauran su, da ‘table settings’.

Farkon da za ki fara sana’ar da kanki ta wacce hanya kika bi wajen ganin kin fara?
Da zan fara dai sai da na tanadi 50k (dubu 50) na ‘registration’, da abin da muka ‘using for a start’. Yadda a ka yi na fara kuma, na amfani da flier ne partypopsby huda. Ina da ‘page’ dina na ‘Business’ a Instagram da Facebook, @partypopsby_huda za a iya samu na ta nan. Farkon farawa ta kuma bayan na sake flier ina dake phone number ina duk na ciki toh ta nan aka neme ni lokacin an yi haihuwa ne ma, ta ce tana son ‘backdrop’ kawai me saukin kudi sai na je na yi mata.

Ya kika ji a lokacin da kika fara kasancewar shi ne farkon fara sana’ar ki, kuma ya kwalliyar wajen ta kasance shin ta samu lambar yabo ko kuwa?
Na ji dadi sosai gaskiya saboda kamar ‘a dream come true’ ne a gurina, yau ga shi na yi aiki na da kaina kuma an yaba sosai.

Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta cikin wannan sana’ar?
Gaskiya akwai kalubale musamman wadanda kuke tare da su sai suna cewa, shikenan tun da kin iya a ‘ebent’ di na ko a na wani na za ki yi mana shikenan mun huta, ba sa tuananiin komai sai ka je ka siyo sannan ka yi, sun dauka kawai komai kana da shi, kawai zuwa za ka yi ka yi musu. Ko kuma mutum ya tambaye ka kudin aiki sai ya ce ya yi tsada ba zai iya ba.

Toh wanne irin nasarori kika samu game da wannan sana’a?
Nasarori suna gaba In sha Allah.

Me kike son cimma game da sana’ar ki?
Ina son in zama sananniyar ‘ebent decoration plug’ a Bauchi, ba Bauchi kadai ba ma ya zamana ko ina an sanni.

Fatima

A ina kike gudanar da ita wannan sana’a, shin kina da wani waje ne na daban da kika ware dan ita sana’ar ko kuwa sai mutum na bukata kike zuwa ki siyo kayan?
A gida nake sana’a ta ban bude wani waje ba, tukunna dai sai nan gaba in sha Allah, ina da kayan aiki na sai dai abin da ba za a rasa ba dole ka siyo.

Ta wacce hanya kike bi dan ganin kin bunkasa kasuwancinki?
Yanar gizo, ita ce hanyar da nake bunkasa sana’a ta.

Ko akwai wadanda kike koyawa sana’ar, idan babu ko kina da sha’awar koyarwa a nan gaba?
A yanzu dai bana koyar wa kowa, amma nan gaba In sha Allah zan yi.

Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi a rayuwarki ba?
Ran da na gama ‘Ahmadu Bello Unibersity Zaria’, shi ne ranar da ba zan taba mantawa ba, ranar da na rabu da ‘friends’ dina na makaranta shi ma ba zan manta da shi ba.

Yaushe za ki yi aure?
Kin san shi Aure da Ajali lokaci ne da su, amma ‘bery soon’ In sha Allah.

Wanne irin namiji kike son aura?
Ina son namiji mai tausayi da addini.

Me za ki ce da Mata na gida musamman wadanda suke zaune ba tare da wata sana’a ba, wacce shawara za ki ba su?
Su tashi su nemi sana’a, saboda sana’a tana da mahimmanci sosai, ko aure kika yi ba ki da sana’a za ki ga ana yawan samun matsala amma idan kina da abun yi an fi zama lafiya.

Wacce shawara za ki bawa mata na gida masu jiran miji?
Ka da su zauna haka nan ba sa komai, su tashi su nemi sana’a har Allah ya kawo musu nagari.

Mene ne burinki na gaba?
Burina shi ne in zama sannanniya, babbar ‘ebent planner’, In sha Allah.

Ko kina da wa ta shawara ko dan tsokaci da za ki ga sauran ‘yan`uwa masu sana’a?
Su rike amana da gaskiya,su rinka hakuri kuma da ‘customers’.

Wanne kira za ki ga masu kokarin fara sana’a?
Su daure, farkon fara wa akwai ‘challenges’ sosai, dole sai kayi hakuri, Allah ya taimake mu baki daya.

Me za ki ce ga makaranta wannan shafi na Adon Gari?
Ina godiya da kuma yi musu fatan alkhairi su ci gaba da karanta shafin nan.

Me za ki ce da ita kanta LEADERSHIP Hausa?
Ina godiya da kokarin da suke yi na daukar labarai masu mahimmanci, Allah kuma ya kara musu daukaka.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Eh! Mamana Babana da kuma Anty na, da addu’a da kuma kwarin gwuiwan da suke bani a ko da yaushe, Allah ya saka musu da mafificin alkhairi ya basu aljannah, sai abokan arziki da ko da yaushe suke min addu’a da fatan nasara. Na gode sosai Allah ya bar zumunci.

Muna godiya Malama Fatima
Ni ma na gode.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Sandan Birnin Milan Sun Ba Wa Dan Wasa Bukayoko Hakuri

Next Post

Me Ya Sa Kano Pillars Ta Fada Ajin Gajiyayyu A Nijeriya?

Related

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata
Ado Da Kwalliya

Gyaran Jiki Da Kyawun Fata

4 days ago
Abin Da Ya Dace Ki Yi Yayin Haila Da Bayan Kin Gama?
Ado Da Kwalliya

Abin Da Ya Dace Ki Yi Yayin Haila Da Bayan Kin Gama?

1 week ago
Ciwon Mara Lokacin Al’ada
Ado Da Kwalliya

Ciwon Mara Lokacin Al’ada

1 week ago
Maganin Kurajen Fuska
Ado Da Kwalliya

Maganin Kurajen Fuska

4 weeks ago
Me Ke Sa Amare Yin Watsi Da Kwalliya Idan Sun Kwana Biyu A Gidan Miji?
Ado Da Kwalliya

Me Ke Sa Amare Yin Watsi Da Kwalliya Idan Sun Kwana Biyu A Gidan Miji?

1 month ago
Maganin Karin Kiba
Ado Da Kwalliya

Maganin Karin Kiba

1 month ago
Next Post
Me Ya Sa Kano Pillars Ta Fada Ajin Gajiyayyu A Nijeriya?

Me Ya Sa Kano Pillars Ta Fada Ajin Gajiyayyu A Nijeriya?

LABARAI MASU NASABA

Yunkurin Philippines Bai Kai Gaci Ba A Tekun Kudancin Kasar Sin 

Yunkurin Philippines Bai Kai Gaci Ba A Tekun Kudancin Kasar Sin 

May 28, 2025
Babu Wata Sauran Mafaka Ga ‘Yan Ta’adda, In Ji Shugaban Rundunar Sojin Sama

Babu Wata Sauran Mafaka Ga ‘Yan Ta’adda, In Ji Shugaban Rundunar Sojin Sama

May 28, 2025
Kamfanoni Mallakin Gwamnatin Sin Sun Samu Bunkasa Bisa Daidaito Cikin Watanni Hudu Na Farkon Bana

Kamfanoni Mallakin Gwamnatin Sin Sun Samu Bunkasa Bisa Daidaito Cikin Watanni Hudu Na Farkon Bana

May 28, 2025
Gwamnatin Adamawa Ta Fitar Da Naira Biliyan 2.4 Domin Biyan Jarrabawar WAEC Da NECO

Adamawa Ta Amince Da Mafi Ƙarancin Albashi Na ₦70,000 Ga Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi 

May 28, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya

Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya

May 28, 2025
An Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Taron Kolin ASEAN-Sin-GCC

An Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Ta Taron Kolin ASEAN-Sin-GCC

May 28, 2025
An Kama Sojoji 18 Da ‘Yansanda 15 Da Suke Siyar Da Makamai Ga ‘Yan Ta’adda

An Kama Sojoji 18 Da ‘Yansanda 15 Da Suke Siyar Da Makamai Ga ‘Yan Ta’adda

May 28, 2025
Taron Kolin ASEAN: Sin Da GCC Na Da Matukar Muhimmanci

Taron Kolin ASEAN: Sin Da GCC Na Da Matukar Muhimmanci

May 28, 2025
Gwamnatin Kano Ta Yi Barazanar Hukunta Matasa Masu Janyo Rikice-Rikice

Gwamnatin Kano Ta Yi Barazanar Hukunta Matasa Masu Janyo Rikice-Rikice

May 28, 2025
Mutum 1 Ya Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Abuja

Mutum 1 Ya Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Abuja

May 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.