Dan Takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso a shirye yake ya karbi Hon. Alasan Ado Doguwa a sansanin siyasar sa.
Hakan ya fito ne daga bakin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Rano, Bunkure da Kibiya a wata hira da manema labarai a Kano.
“Hon. Doguwa, yayi ikirarin cewa, jagoranmu (Sanata Kwankwaso) ya kafa wani kwamiti mai wakilai 4 domin zuwa jajantawa Doguwa, karkashin jagorancin Sanata Rufa’i Sani Hanga tare da ni (Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum) da shugaban jam’iyyar mu na jiha, Hon. Umar Haruna Doguwa da Hon. Sarki Aliyu Daneji”
Ya ce, Siyasa tsari ce mai bukatar adadin jama’a da mabiya, a shirye muke mu yi sulhu don sake hadewa da tsofaffin abokanmu a yunkurinmu na ganin mun cimma sabuwar Nijeriya.
“A lokutan baya, yawancin mu mun kasance cikin jam’iyyu daban-daban da Mai Girma Engr. Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso amma bayan fahimtar kyawawan kudurinsa a siyasance sai muka sake hadewa da shi a jam’iyyar NNPP kuma ina tabbatar muku cewa muna cikin nutsuwa sosai a yanzu fiye da kowane lokaci.”