Shugaban Ukraine, Bolodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar kasarsa, wajibi ne a sanya kasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki.
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Bolodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Bladimir Putin, idan har hakan ne zai kawo karshen yakin da suka kwashe kusan shekara uku suna gwabzawa.
Sai dai shugaba Zelensky ya sake nanata bukatarsa ta karin makamai domin ci gaba da samun nasara kan Rashar.