Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye kasarsa take ta inganta hadin gwiwa da hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO), domin sa kaimi ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.
Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da Audrey Azoulay, darakta janar ta hukumar a babban dakin taron jama’a, dake birnin Beijing.
- CMG Ta Kaddamar Da Bikin Fara Nuna Shirin “Journey Through Civilizations” A Hong Kong Da Macau
- Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Ba Da Lambar Yabo Ga Ayyukan Ba Da Ilmi Ga Yara Mata Da Mata Na UNESCO Na Shekarar 2023
Shugaban ya ce Sin ta kasance mai goyon bayan ayyukan UNESCO a ko da yaushe, kuma UNESCO ta aiwatar da kyawawan ayyuka da zummar kare zaman lafiya da inganta ci gaban duniya. Yana mai cewa, irin wannan hadin gwiwa na da matukar daraja kuma ya kamata ya dore. Har ila yau, a shirye Sin take ta hada hannu da UNESCO wajen bayar da gudunmuwarta ga ci gaban duniya na bai daya.
Da take yabawa goyon bayan da Sin ke ba ayyukan UNESCO, Audrey Azoulay ta tabo shirin lambar yabo ta ilimin mata da ‘yan mata da aka kafa bisa hadin gwiwar Sin da UNESCO, tana mai cewa, ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ilimin mata da ‘yan mata a fadin duniya.
Ta ce bisa kyakkyawan hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, hukumar na fatan karfafa musaya da hadin gwiwa da Sin a bangarorin da suka hada da kare al’adun da aka yi gado da kimiyya da al’adu da fasaha da kara cimma matsaya guda tsakanin kasashen duniya da bayar da gudunmuwa wajen kare zaman lafiya da ci gaban duniya. (Fa’iza Mustapha)