Yau Juma’a ranar 29 ga wata ne, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya gudanar da wani biki don kaddamar da nune-nunen “Journey Through Civilizations” wato hanyar fahimtar wayewar kai, a lokaci guda a yankunan musamman na Hong Kong da Macau na kasar.
Mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong ya ba da jawabi ta kafar bidiyo cewa, a matsayinsa na wayewar kai daya tilo a duniya da ke ci gaba da wanzuwa har zuwa yau, kuma bai taba katsewa ba, wayewar kan kasar Sin ya tara jigon wayewa mafi tsawo da dadewa a cikin dogon tarihin dan Adam. Kuma bisa kyakkyawan tsarin da shawarar wayewar kai ta duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, jama’ar kasar Sin suna aiki tukuru don gina wayewar kan al’ummar kasar na zamani, da sa kaimi ga bunkasar wayewar kan dan Adam.
Shen Haixiong ya yi maraba da abokai na Hong Kong da Macau da su shiga ayyukan nuna shirin “Journey Through Civilizations”, don kara fahimtar wayewar kan kasar Sin, da al’adun kasar masu tsawon shekaru dubu biyar, da kara amincewa da kasar da girmanta, da kuma sa himma wajen shiga yunkurin neman ci gaban kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)