Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya shaida cewar dukkanin shirye-shiryen yin gyaran fuska ga dokar zabe zai kammalu kafin lokacin zabukan 2027.
Ya shaida hakan ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin, ya karyata jita-jitan da ke yawo na cewar an koreshi daga shugaban hukumar, ya tabbatar cewa shi ne shugaban hukumar zabe har yanzu.
- Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027
- 2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC
Shugaban INEC wanda ke amsa tambayoyin manema labarai a yayin da ya shigo cikin tawaga domin shaida rantsar da kwamishinan hukumar zabe ta kasa su biyu da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.
A cewarsa, hukumar da sauran masu ruwa da tsaki sun sake zama domin nazartar babban zaben 2023, kuma sun fito da shawarori guda 142, ya kara da cewa daga cikin wadannan shawarorin, takwas suna bukatar gyara ga dokar zabe.
Farfesa Yakubu, wanda ya ce ya halarci fadar shugaban kasa ne domin kaddamar da kwamishinonin hukumar guda biyu daga Kudu maso Gabas da Arewa maso Yamma, ya ce a yanzu hukumar ta samu cikakkun kwamishinonin kamar yadda doka ta tanada.
Dangane da sake fasalin dokar zabe, shugaban hukumar INEC, ya ce hukumar na yin cudanya da majalisar dokokin kasar, inda ya ce makwanni biyu da suka gabata, ta yi wani taro a Legas tare da kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan sake fasalin zabe.
“Majalisar dokoki ta kasa za ta shirya taron jin bahasin jama’a, bayan nan za a samar da kudirin doka, a karshen zancen za a mika wa shugaban kasa domin sanya hannu,” ya
shaida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp