Nijeriya na fuskantar kamfa a waklicin mata a mukaman siyasa a matakai daban-daban abin kuma yana matukar damun masu ruwa da tsaki.
Idan muka leka zauren majalisun kasa za a iya fahimtar yadda lamarin ya tabarbare.A majalisar tarayya ta 10, na da waklilai 3 ne kacal na mata a cikin ‘yan majalisa 109 a majalisar dattawa kuma, wanda yake nuna kashi 2.7 na daukacin ‘yan majalisar.
- Shugaban Zanzibar Ta Tanzania: Ba Za Iya Raba Ci Gaban Afirka Da Sin Ba
- Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi
Yayin da kuma a majsalisar wakilai ake da mata 17 kawai a cikin mambobi 360 da muke da su wanda ke nuna kashi 4.7 na daukacin ‘yan majalisar, gaba daya a cikin yawan ‘yan majalisun da muke da su da suka kai 469 kashi 4.2 kacal ne matan Nijeriya suka iya darewa a kakar siyasar da ta gabata.
A majalisa ta 9, an samu ‘yan majalisar dattawa 8 kashi 7.3 yayin da aka samu ‘yan majalisar wakilai 13 mata wanda hakan ke nuna kashi 3.6 gaba daya an samu kashi 4.5 a majalisar tarayya a majalisa ta 9.
A matakin majalisun jihohi, mata basu tabuka wani abin a zo a gani ba. Rahottani sun nuna cewa, a cikin majalisun jihohi 15 ba a samu wakilcin wata mace ko daya ba, a jihohin da aka samu mata sun ci zabe kuma basu da yawan a zo a gani. Wadannan alkalumma ba abin a yi maraba da su ba ne kuma babu wata al’ummar da za ta ci gaba yayin da aka ki tafiya da mafi yawan al’ummar ta a bangaren siyasa da tattalin arziki.
Mun yi imanin cewa, wannan babban kalubale ne, a wasu kananan kasashen Afirka an samu bunkasa da karuwa a wakilcin mata a majalisun dokokinsu da sauran mukaman gwamnati.Misali a kasar Rwanda an samu kashi 61 na mata a majalisar kasar. Afirka ta Kudu na da kashi 46.23 na mata, Senegal na da kashi 46.06 yayin da kasar Namibia ke da kashi 44.23 na mata a majalisunsu. Hatta ma kasar Somaliya da yaki ya daidaita nada wakilicin mata a majalisarta da suka kai kashi 20.
Wannan abin takaicin ya karfafa kungiyoyin fararen hula masu fafutukar kwato ‘yancin mata, su zafafa kokarin da suke yi na samar da karin mata a matakan siyasa daban-daban a kasar nan, amma har yanzu hakar tasu bata kai ga cimma ruwa ba.
A shekarar da ta gabata majalisar kasa da maza suka yi wa babakere an yi watsi da shirin yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima inda aka nemi aware wa mata kashi 30 na kujerun majalisu a matakin tarayya da jihohi.
Amma duk da haka ana ci gaba da fatutuka ta hanyar amfani da sabon salo inda wasu kungiyoyi masu fafutuka suka shirya jawo hankalin Majalisar tarayya a kan bukatar su goyi bayan karin mata a majalisar tarayya ta hanyar yi wa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima don cimma ita manufar.
Muna bada goyon mu ga duk wani kokari na kara karfafa tagomashin mata a harkar siyasar Nijeriya, musamman ma matakan da ake kokarin dauka a majalisar dokokin kasa.
Muna sane da tarnakin da mata ke fuskanta wajen cimma ma brinsu na siyasa wadanda suka hada da banbancin da ake nuna masu saboda kasancewarsu mata da kuma wasu al’adun gargajiya.
Muna kuma sane da cewa, mata na fuskantar matsalolin rashin kudi a yanayin siyasar Nijeriya da aka bayar da muhimmanci a kan kudi wajen gudanarwa.
Amma kuma ya zama dole Nijeriya ta yi watsi da wadannan kalubalen ta kuma rage tasirin kudi a harkar siyasar kasa. Ya kuma kamata a yaki al’adar tashin hankali a siyasa musamman ganin mata ba sa iya jure tashin-tashina da ake dangantawa da siyasa. Wani dalili da ya sa mata ke nisanta kansu daga siyasa kuma shi ne yadda aka haifar da kyamarsa ga mutane, ana nuna tamkar mara sa mutumnci ne ke shiga siyasa.
A a mastayinmu na gidan jarida muna maraba da kokarin uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu na karfafa shigar mata harkokin siyasa a Nijeriya.
A taron da aka yi kwanan nan na kungiyar kawancen tattalin arziki ta Afirka ta yamma ECOWAS a Abuja, ta bayyana a zaman taron cewa, lokaci ya yi da za a karfafa shigar mata a siyasar yankunan Afirka ta Yamma, duk da ta tabbatar da irin tarnaki da matsalolin da mata ke fuskanta a siyasar yankin saboda mastayin su na mata.
Ta kuma kara da cewa, “A yau ana tuna mana tsananin bukatar samar da hanyoyin kawo karshen bangarancin da ake nuna wa mata a tsarin siyasar kasar nan. Duk da ci gaba da ake samu har yuanzu a kwai matsallolida ke takura wa mata samun manyan mukaman siyasa a Afirka.
Matsalolin sun hada da al’adun al’umma da yadda ake tsara tafiyar da siyasar da kuma rashin kudi a tsakanin matan mu.
“An gano cewa, tsarin ayyana kujeru ga mata yana karfafawa yadda matan ke shigar siyasar, har su samu mukamai a majalisun jihohi da na tarayya. Kasashe irin su Sweden, Norway da Spain sun yi amfani da irin wannan tsarin sun kuma yi nasarar kara yawan mata a majalisun wanda ya kara wakilcin mata a matakan majalisun kasar su.
“idan muka duba yadda kididdiga ta kasance a duniya gaba daya, za mu iya fahimtar yadda kasashe suka yi amfani da tsarin ayyanna kujera wajen kara yawan mata a majalisunsu. Wannan ne yake karfafa mana bukatar kungiyar ECOWAS ta yi amfani da wancan salon wajen cimma wannan manufar, ta yadda za a samu karin mata a majalisun dokin mu gaba daya.
Duk da mun yi imanin cewa, a kwai bukatar yi wa tsarin mulki kwaskwarima wajen cimma karin mata a madabun iko a majalisun mu, amma dole suma matan su canza tunaninsu a kan yadda suke fuskantar harkar siyasa. Tabbas mata manya da kanana suna da masaniya cewa a harkoin siyasa ya kamata su rika tunanin ba suna zaune bane, za a zo a basu mukami ba tare sun fafata ba, dole mata su fito su yi gwagwarmaya tare da ‘yan uwan su maza domin cimma burinsu na siyasa.
Burin samar da kashi 30 na mata a majalisun Nijeriya abu ne mai yiwuwa da zarar sun kuduri aniyar yin haka, amma kuma dole ne su samarwa kansu cikakken tsarin cimma wannan burin.