A yau ne aka fara bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na Sin ko Canton Fair karo na 135 a birnin Guangzhou, wanda zai kai har zuwa ranar 5 ga watan Mayu.
An yi wa baje kolin taken “Samar da ingantaccen bunkasuwa da bude kofa a babban mataki”.
Kuma za a gudanar da shi a matakan nune-nune guda uku, kowane mataki zai dauki kwanaki biyar. Adadin yankin baje kolin ya kai murabba’in mita miliyan 1.55, tare da wuraren baje koli 55 da jimillar rumfuna 74000. Akwai kusan kamfanoni 29000 masu shiga baje kolin. Ya zuwa jiya, masu sayayya guda 149000 daga kasashe da yankuna 215 sun riga sun yi rajista, wanda ya kasance gagarumin karuwar kashi 17.4 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarun baya. (Mai Fassarawa: Yahaya Mohammed)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp