A yanayi mai saurin canjawa irin na yau, mutane suna mayar da hankalinsu sosai kan aiki, domin zaman rayuwarsu.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba gargadin Sinawa da cewa, kada su manta da iyalansu a yayin da suke shan aiki.
A yayin bikin tsakiyar yanayin kaka, wato a lokacin da Sinawa ke haduwa da iyalansu, Xi Jinping ya ce, makomar iyali da ta kasa suna da alaka sosai, don haka ya kamata a hada tabbatar da mafarkai na daidaikun mutane da na iyali cikin mafarkan kasa da na al’umma. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp