Wani abokina ya taba zuwa kasar Benin yau da shekaru da suka wuce, bayan da ya dawo gida, ya kan tuna da abarbar kasar ta Benin mai dadin gaske.
A kwanakin da suka wuce, abokin nawa ya yi matukar farin ciki, inda ya gaya min cewa, an amince a shigo da abarbar kasar Benin kasuwar kasar Sin, don haka ma zai samu damar dandana su a gida ba tare da yin doguwar tafiya har zuwa Benin ba.
- Dandalin Hongqiao Na Maida Hankali Ga Kiyaye Tsarin Cinikayyar Sassa Daban Daban
- CIIE Na Da Matukar Muhimmanci Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
Abarba na daga cikin muhimman nau’o’in amfanin gona da ake samarwa a kasar Benin, wanda ake mata kirarin “Burodi mai zaki na Afirka”, sakamakon irin dandanonta na musamman. A yayin da shugaban kasar Benin ya kawo ziyara kasar Sin a watan Satumban bana, kasashen biyu sun daddale yarjejeniya game da shigowa da abarbar kasar Benin cikin kasuwar kasar Sin.
Watanni biyu kacal, an fara ganin abarbar Benin a gun bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) karo na shida da yanzu haka ke gudana a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, wadda ta yi matukar janyo hankalin al’umma. A game da wannan, jakadan kasar Benin a kasar Sin, Simon Pierre Adovelande ya bayyana cewa, “ina fatan masu sayayya na kasar Sin za su kara fahimtar abarba mai dadi ta Benin, kuma muna fatan samun ’yan kasuwar kasar Sin da za su kai abarbarmu zuwa kasuwar kasar, har ma da teburin al’ummar Sinawa.”
A cikin ’yan shekarun baya, kasar Sin ta yi ta sa kaimin shigowa da kayayyaki masu inganci na kasa da kasa, don duniya ta more babbar kasuwarta da ma ci gabanta. Abin lura shi ne, kasar Sin ta bullo da wata kafar musamman ta shigowa da amfanin gona na kasashen Afirka, don tallafawa kasashen Afirka wajen fitar da karin amfanin gonarsu. Avokado na Kenya da barkono na Ruwanda da Lemo na Afirka ta Kudu da wake na Tanzania, har ma da Abarba na Benin, na daga cikin karin kayayyakin kasashen Afirka da suka samu damar shiga babbar kasuwar kasar Sin, wadanda a sa’i daya suka kyautata rayuwar al’ummar Sinawa, a sa’i dayan kuma, suka taimaka ga ci gaban tattalin arzikin kasashen da suke fitar da kayayyakinsu.
Bana ake cika shekaru 45 da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, kana shekaru 10 da Sin din ta gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, haka kuma shekara ta shida da kasar ta shirya bikin baje kolin kayayyaki da ake shigowa da su kasar Sin, bikin da ya kasance irinsa na farko a duniya da ke mai da hankali musamman a kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare. A yayin da farfadowar kariyar ciniki da ra’ayin cacar baka ke haifar da barazana ga dunkulewar tattalin arzikin duniya, yadda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka a kan bude kofarta ga ketare, da ma kawar da shingen ciniki tare da kasashen da suka karbi shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, ya shaida niyyarta wajen ganin an tabbatar da ci gaban bai daya na kasa da kasa, haka kuma ya bayyana ma’anar “Gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam” da ta gabatar. (Mai Zane:Mustapha Bulama)