Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Sunusi Hafiz, wanda aka fi sani da Sunusi Oscar 442 a matsayin mataimakinsa a kan masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood.
Oscar, mai shekara 46 a duniya ya shafe shekara sama da 30 a masana’antar Kannywood inda kuma ya shirya fina finai da dama.
Kwararre ne wajen shirya fina finai da bayar da umarni sannan ya dade yana fafutukar ganin an kawo gyara a masana’antar.
Shi ne ya shirya shahararun fina finan nan na Ummulkhairi da Dawud da kuma Yanayi da suka dade ana maganar su a kasar hausa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp