Dan takarar gwamnan a jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf wanda akafi sani da Abba Gida-gida, ya zargi shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas da amfani da ‘yandaba wurin kai wa ‘yan takara ‘yan jam’iyyar adawa hare-hare.
Abba Gida-gida, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin tabbatar da zaman lafiya da cibiyar AMG tare da hadin gwiwar jami’an rundunar tsaro ta ‘yansandan jihar Kano suka shirya.
Dan takarar ya bayyana yadda aka kai masa hari sau biyu jim kadan bayan gama taron rattaba hannu kan zaman lafiya da aka gudanar a dakin taro na Jami’ar Bayero da kuma dakin taro da ke mumbayya House a lokacin zaben da ya gabata na shekarar 2019.
“Muna da shaidu na ganin ido da bidiyo kan yadda Abdullahi Abbas ke amfani da ‘yandaba wurin kai wa ‘yan takarar siyasa da ke jam’iyyar adawa hare-haren ta’addanci” inji Gida-gida.
A karshe, ya daura alhakin kawo karshen hare-haren ta’addancin kan jami’an tsaro musamman na hukumar ‘yansandan jihar, inda yace, su kadai ne za su iya maganin masu daukar nauyin ‘yandaban da ke kai hare-haren.