Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya sanar da Julius Ihonvbere (Edo) a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar da kuma Usman Kumo (Gombe) a matsayin mai tsawatarwa na majalisar.
Abbas kuma bayyana Halims Abdulahi daga Kogi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye da Oriyomi Onanuga daga Ogun a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.
- Akpabio Ya Nada Bamidele, Ndume, Umahi Da Asiru Manyan Mukamai A Majalisar Dattawa
- Mutanen Da Ke Aiki A Karkashina Na Da Gidaje A Kasashen Waje, Amma Ba Ni Da Gida A Waje -Dangote
Kakakin majalisar dai, ya sanar da Kingsley Chinda (PDP, daga Ribas) a matsayin shugaban marasa rinjaye; sai Ali Isah (Gombe) bulalan marasa rinjaye; sai Madaki Aliyu (NNPP, daga Kano) a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye da George Adegeye (LP, Legas), mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Abbas ya bayyana hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp