A ziyarar da wakilinmu ya kai zuwa gidan Dirama, idanunsa ya gane masa abubuwa daban-daban, sannan kunnensa ya jiye masa wasu daga ciki. Akwai abubuwan ban mamaki da ban tausayi gami da ban al’ajabi.
Abubuwan ban mamaki
Daga cikin abubuwan da ya gani na ban mamaki su ne, cin karo da cikakkiyar budurwa wacce da ka kalleta ba sai an yi maka bayani ba ka san gidansu akwai rufin asirin da ba rashi ne ko talauci ya kawo ta gidan ba, sannan kuma kuma za ka ga budurwar da idanka dube ta ka san ba rashin masoyi ne ya kawo ta wannan wuri ba, saboda irin kyan halittar da Allah ya yi mata.
- Dalilin Da Ya Sa Gwamnati Ta Fara Raba Wa Manoma Kayan Adana Amfanin Gona -Sakatare
- Marigayiya Hajiya Murja Bara’u Mangal: Uwa Tagari
Wata kuma za ka ganta ita ba kyau ba, babu cikakkiyar sutura sannan kuma ga kwarewa a tantiranci, domin a ganinta idan ba ta yi irin wannan zakewar ba kamar ba za ta samu kasuwa ba.
Abin Tausayi
Wani abin tausayi da zai iya sanya hawaye ko kuka shi ne, cin karo da yarinyar da bai kamata a ce an ganta airin wannan wuri ba, wannan ya hada kankantar shekaru, da kuma yunkurin ganin sai kwatanta abin da na gaba dai ta ke yi, mafi muni shi ne, wadanda suke da halayya ta neman mata, ko kuma mazinata su ne ke ta kokarin ganin sun kusance ta.
Za ka ga mutum wanda a haife ya yi jika da ita, amma ba shi da burin da ya wuce ya ga kusance da kwanciya.
Wakilinmu ya ce ya taba ganin yarinyar da duka-duka shekarunta ba su haura 12 zuwa 23 ba wacca saboda kankantarta ma in ban da aiken ta ba a bin da ake iya yi, amma wasu kuma kullum bukatarsu su ga sun kawar da ita.
Ba wannan ne ya bani mamaki ba, yadda a wasu lokutan za ka ga tana rike da karan taba sigari a hannunta tana zuka, hakan na nuni da ita ma ta fara hawa kan turba kenan.
Wani babban abin tausayi da ya gani a mazowa gidan domin aiwatar da sana’arsu shi ne, ganin masu manyan shekaru daga sashen wasu mata da har yanzu basu san Annabi ya faku ba a gidan suna zuwa kallon yadda yara matasa ke cashewa madadin su tub asu koma ga Allah.
Abin takaici da kaico
Wani abin da zai baka takaici kuma shi ne, Gidan Dirama ba gida ne da tsofaffin karuwai ke kwana ba, a a duk wacce ka gani in ma dai budurwa ce ta baro gidan iyayenta, ko kuma a a bazawara ce mai kuruciya da idan ba ta gaya maka ba ba za ka san sirrinta.
A halin yanzu mafi aksarinsu ba suna baro gida ne domin za a yi musu auren dole kamar a da can ba, a a suna fita ne domin sun fi karfin iyayensu su fada musu su ji, wasu ma suna fita ne da izinin iyayen domin su iyayen sun san ko da sun fada ba za su ji ba.
Wakilimmu ya samu zantawa da wata uwar ‘ya’ya uku ‘yan mata biyu da namiji daya da ta nemi a sakaya sunanta, wadda daya daga cikin ‘ya’yan nata ta fita zuwa irin wannan gida na Dirama, inda ta bayyana masa cewa, ita ce ta bar yarinyar zuwa wannan gida.
“Gaskiya ni ce nake barinta ta je don kai na, dalili kuwa shi ne, gara dai ko me za ta yi nasan tana dawo wa gida ai zan san halin da take ciki fiye da a ce ta fita ina fushi da ita, kuma ta ki dawowa gida.
“Ka san yaron yanzu ka haife shi ne amma ba ka haifi halinsa ba, ai ina nan zaune take kawo min labarin wasu suna shafe shekara da shekaru ba su dawo gida ba. Ita dai ‘yar uwarta ka ga tana zuwa makaranta ta addini da ta Boko amma dai ita waccan mu nan muna ta addu’a Allah ya shirya mana, na yi kuka a farkon lamarin har na hakura sai dai‘yar uwarta ta ce ba ni hakuri, amma dai ban taba yi mata baki ba,”in ji ta.
To ko yaya ‘yan uwan irin wadannan‘yan mata ke ji a ransu yayin da aka ce ‘yar uwarsu ta shiga irin wannan yanayi? Aminu wa ne ga ita wannan yarinya, ya bayyana wa wakilimmu irin halin da ya tsinci kansa lokacin da ya shigo ya samu mahaifiyarsu na kuka.
“Hankalina ya yi matukar tashi da na shigo gida na samu ummanmu tana kuka, abin da ban saba gani ba, da na tambayi daya kanwar tamu ta fada min abin da yake faruwa, na ji kamar raina zai fita, ana cikin haka sai ga ta ta shigo,babarmu ba ta taba hana ni abu na ki ba amma a ranar da fara dukanta ban ma san tana cewa na bari ba, kuma daga ranar har yanzu ba na yi mata Magana idan ta zo gida,” in ji shi.
Yadda ake gudanar da wasa a gidan a gidan Dirama
Wasannin da ake gudanarwa a gidan ya kasu kashi biyu, wani gidan su kan yi da yamma kuma su yi daddare, wasu kuma sai daya suke yi a rana, wato da daddare kawai.
Ana fara was an bayan Sallar Isha’i, ta yadda za ka ga ‘yan matan gidan sun caba ado sosai, an sanya kida yana tashi gidan kamar ya yi girgiza. Daga nan kuma za ka ga samari na barkowa ta ko ina domin halartar gidan.
Bayan gidan ya yi cikar kwari, sai a samu daya daga cikin masu gabatarwa ya fita da abin magana yanayi wa mahakarta gidan barka da zuwa, sannan zai umarci dukkan ‘yan matan gida da su taho kan babban wani dakali da ake cashe rawa, bayan sun hallara kowa ya gansu, sai kuma ya uamarce su da su je su gaida jama’ar da suka zo domin kallo.
Daga nan ne ‘yan matan za su fantsama cikin jama’a domin gaishe su, a nan ma wata ta kan samu sabon saurayi wanda a lokacin da take cashe rawa zai yi mata liki.
Bayan sun gama da gaisuwar, sai ya sake umartar su da su dawo wannan wuri ta inda za a fara zabar ‘yan matan daya baya daya suna hawa ana sanya musu waka suna kwaikwayon wakar da saurayi kamar dai yadda ake a fim, kuma kowacce dai irin wakar da take so da zarar an sa to duk wanda ya saba zuwa gidan ya san wannan wakar ta wance ce.
Haka su ma mazan suke kowa da tasa wakar, daga nan ne sai samari su fara zuwa suna liki. To wacce ta fi samun kudi za su fara gasa da ta biyunta, a rawa domin a ga wacece ta fi kowacce tara kudi, nan dai za a yi tara kudi.
Amma wacce aka ga ba ta da kowa, sai a fito dai ta kan wannan dabe a ba da sanarwar cewa idan har ba a samu mai fansarta da kudi ba, to za a jika ta da ruwa, kuma za a kawo jakar Fiya wota guda a rirrike, idan aka kirga, 10 babu wanda ya zo yaya yi mata liki, daga nan ne za a fara jika da ruwa har sai jike sharkaf.
To a nan ne idan ta yi dace da masoyi ko kuma wani ya tausaya mata, sai ya zo ya fanshe ta da wani adadin kudi.
Rayuwar wayewa ko kaskanci?
Mutum ya kan fahimci irin rayuwar da suke wacce ba sai an gaya masa ba, idan ya kalli inda suke kwana da sauran mu’amalolin yau da kullum. Kango ne da aka gewaye shi da Katanga, daga ciki kuma an yi musu dakunan kwana, wasu gidajen Diramar dakunansu na katakwaye ne da aka gewaye da kwanonrufi da ake cewa (Bacha), irin wadanda idan ana tsuga rana za ka rasa inda zaka sa kanka.
Wasu daga cikinsu samarin gidan ne samarinsu, yayin da wasu kuma suke da nasu samarin daga waje. Babu irin nau’in mutanen da ba sa zuwa kallo gidan, wasu suna zuwa domin samun ‘yan mata, yayin da wasu kuma suke zuwa kawai don su nishadantu.
Wasu daga cikin ‘yan matan sun yi nisa a shaye-shayen kwayoyi, wasu ko sigari ba sa sha, wasu babu ruwansu da addini, yayin da za kawata saboda kula da addini kamar ka ce malama. Akwai masu zaman Dadiro da wasu mazan wata kuwa idan ta gama wasan ma a gidan iyayenta take kwana, kamar wacce muka buga misali da ita a baya.
Wasun su su kan je kallon Dambe da yamma, wasu kuwa sun gwammace su zauna su yi wasan Ludo ko karta, kuma ba ‘yammatan Musulmai kadai ke zuwa zaman gidan ba har ma da wadanda ba Musulmai ba Allah ka shirye mu ka shiryi masu ka mayar da su gaban iyayensu cikin salama.