A farkon watan Nuwamba, Ukraine ta bayar da rahoton cewa, an yi ruwan bama-bamai kan kimanin wurare 120 a cikin kwana daya, hari mafi girma tun bayan kamawar wannan shekarar.
Amma duk da haka hankalin duniya ya ci gaba da kasancewa a kan Gaza da Isra’ila.
Yiwuwar samun raguwar daga kasashen duniya, shi ne fargaba mafi muni ga kasar Ukraine tun daga lokacin da Rasha ta kaddamar da mamaya a kanta.
- Rashin Adalci Ne Karbe Kashi 40 Cikin 100 Na Kudaden Shigar Jami’oi (1)
- Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Kwarya-kwaryar Taron Shugabannin APEC
Idan babu tallafin soji da na kudi daga kawayenta, Ukraine ba za ta samu wata dama ba wajen tunkarar Rasha a fagen daga da kuma kiyaye farmaki ta sama, wanda ke da matukar muhimmanci ga kare garuruwan Ukraine.
Bari mu duba wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a fagen daga tsakanin Rasha da Ukraine.
Yakin Juriya
Manazarta da dama sun ce bangaren da zai iya jure wa hasara na tsawon lokaci shi ne zai yi nasara a yakin.
Kwamandan dakarun Ukraine, Balery Zalumzhny ya bayyana yakin a matsayin “mai gajiyarwa.”
“Kamar yadda ya faru a yakin duniya, mun kai wani matsayi na ci gaban kere-kere da za a iya cewa an kai bango,” kamar yadda ya bayyana a wata mukala a jaridar ‘the Economist’ ta Birtaniya.
A wani bayani kan wata biyar da sojojin Ukraine suka kwashe suna kokarin kwato yankunan da Rasha ta kwace, ya ce a tsawon wata biyar, sojojin sun matsa a yankin da bai wuce kilomita 17 ba.
A halin yanzu Rasha na iko da kimanin kashi 17.5% na fadin kasa mallakin Ukraine, duk da an samu sauyi a 2023.
A makonnin da suka gabata fada ya kazanta a kusa da garin Abdiibka da ke gabashin Ukraine, inda dukkanin bangarorin biyu suka yi asarar dakaru ba tare da wata nasarar a zo a gani ba.
Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta yi kiyasin cewa asarar da Rasha ta yi a garin Abdiibka a shekarar 2023 ta fi ta kowane lokaci.
Janar Zalunzhny ya bayyana yadda a yanzu bangarorin biyu ke takama da kayan yaki na zamani, ta yadda kowa na iya ganin abin da abokin hamayyarsa ke kitsawa.
Ya ce sanadiyyar hakan ne dukkanin bangarorin biyu suka kasa samun nasarar a-zo a -gani.
Daga nan sai ya yi kira ga kawayen Ukraine da su samar wa kasar da makamai masu tsananin saiti, da kuma makaman atilare.