Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta ce, masu kona ciyayi ne suka haddasa gobarar da ta tashi a gidan rediyon tarayyar Nijeriya, FRCN da ke Kaduna.
Mataimakin kwamandan hukumar, Ayuba Yohanna ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadin da ta gabata a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Kaduna.
- Masu Sarrafa Waken Soya Na Neman A Haramta Fitar Da Shi Waje
- Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilun 2024 – Minista
A cewarsa, gobarar ta tashi ne daga wani fili dauke da ciyayi da yawa da ke bayan ofishin sayayya na gidan rediyon.
Ya ce, jami’an da ke bakin aiki sun garzaya wurin da lamarin ya faru bayan samun kiran gaggawa da misalin karfe 1:45 na rana.
Yohanna ya ce, ofisoshi biyu na sashen sayan kayayyaki ne lamarin ya shafa ba tare da asarar rayuka ko jikkata ba.
Idan ba a manta ba, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Malagi, ya ziyarci gidan rediyon a ranar Juma’a inda ya yi alkawarin gudanar da gyare-gyare a gidan rediyon da kuma tashar talabijin ta NTA.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp