ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masu Sarrafa Waken Soya Na Neman A Haramta Fitar Da Shi Waje

by Abubakar Abba
3 years ago
Soya

Kungiyar masu sarrafa mai daga waken soya zuwa man girke-girke ta kasa (OSPAN), ta bayyana jarinta na dala miliyan 250 da ta zuba; don sarrafa mai daga Irin Waken Soya, a matsayin wanda ke fuskantar barazana, sakamakon yadda ake fitar da Waken Soyar zuwa kasashen waje.

Wannan korafin na kunshe ne a cikin sanarwar da Shugaban Kungiyar na Kasa, Sama’ila Barau Maigoro da Mataimakinsa, Mista  Hule Idyerkas suka sanya wa hannu tare da fitar da shi a Garin Lafiya da ke a Jihar Nasarawa.

  • Hizba Ta Gana Da Kungiyar Masu Bege, Ta Bukaci Su Tsabtace Harshe
  • Na Fi Jin Dadin Rubutu Da Sassafe Ko Dare – Princess Mazadu

Sanarwar ta yi kira da a haramta fitar da Waken Soya daga Nijeriya zuwa sauran kasashen ketare, domin a karfafa wadanda suke sarrafa Irin Waken Soyar zuwa man girki; kwarin guiwa.

ADVERTISEMENT

A cewar sanarwar, idan aka sarrafa man daga Irin na Waken Soya zuwa man girki, hakan zai bayar da dama wajen sarrafa  ainahin danyen man Waken Soyar da za a rika yin amfani da shi a cikin kasar nan, wanda hakan zai taimaka wajen karya farashin sauran man girki a Nijeriya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, akwai ‘ya’yan kungiyar manya da matsakaita da suka zuba jarinsu, domin sarrafa mai daga Irin Waken Soya zuwa man girki.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Ta kara da cewa, a yanzu haka man girkin da ake sarrafawa daga Irin Waken Soya a kowace shekara; ya kai tan miliyan uku, inda kuma jarin da aka zuba a fannin ya kai na kimanin dala miliyan 250.

A cewar sanarwar, a yanzu haka mune a kan gaba wajen samar da aikin yi a bangaren aikin noma na fadin kasar nan, domin muna samar da ayyuka na kai tsaye sama da 200,000.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, muna so Shugaban Kasa Bola Ahmed  Tinubu da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Doris Uzoka-Anite su sani cewa, akasarin masana’antun da ke sarrafa mai daga Irin Waken Soya zuwa man girke-girke a kasar nan, na ci gaba da kullewa sakamakon karancin kayan aiki, musamman Waken Soya.

Bugu da kari sanarwar ta bayyana cewa, Manoman Waken Soya a shekarar 2022; sun noma Waken Soya kimanin tan 680,000, amma maimakon su sayar da shi ga masu sarrafa shi a nan cikin gida, sai suka gwammace fitar da shi zuwa kasashen ketare; domin samun kazamar riba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, wannan lamarin na ci gaba da zama babbar barazana ga tattalin arzikin wannan kasa tare da jawo koma baya ga kokarin da gwamnatin kasar ke yi na fadada tattalin arziki da kuma kokarin samo wadanda za su zuba hannin jari a fannin tattalin arzikin tare da samar da ayyukan yi a fannin sarrafa Irin Waken Soya zuwa man girki.

Kungiyar ta sanar da cewa, Nijeriya ba ta cikin jerin kasashen duniyar da ke a kan gaba, wajen noman Waken Soya, inda wannan sabon halin na fitar da Waken Soya zuwa ketare ke jawo wa masu sarrafa mai daga Irin Waken Soya a kasar nan babban koma baya.

Kazalika, kungiyar ta OPSAN ta bukaci Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ta kawo musu daukin gaggawa a kan matsalar fitar da wannan Wake na Soya da ake yi zuwa kasashen waje.

Sannan, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta haramta fitar da Waken Soyar na wucin gadi daga nan Nijeriya zuwa sauran kasashen waje, har sai an tabbatar an samar da wadatuwarsa a fadin wannan kasa baki-daya.

Har ila yau, kungiyar ta kara da cewa, idan aka haramta fitar da Waken Soyar daga wannan kasa zuwa kasashen ketaren na wucin gadi, hakan zai taimaka wajen kara fadadawa da kuma bunkasa masana’antun da ke sarrafa Irin Waken Soyar zuwa na man girki a kasar nan tare da kara bunkasa tattalin arziki da kara samar da ayyukan yi  ga ‘yan kasa baki-daya.

Soya
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Kula Da Tsaftar Hakori

Kula Da Tsaftar Hakori

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.