Yayin da ake fafutukar neman gurbin zagaye na 32 na gasar Uefa Europa League mayan kungiyoyin kafa biyu As Roma da FC Porto zasu kara a filin wasa na Estadio Do Dragao dake birnin Porto na ƙasar Portugal, ana hasashen wasan zai matukar ƙayatar duba da cewar duka kungiyoyin biyu babu kanwar lasa a cikinsu.
Duk wanda ya samu nasara a wasan zai haɗu da Athletico Bilbao ko SSC Lazio a wasan zagaye na 16, FC Porto sun samu nasara a wasanni biyar kacal a cikin wasanni 25 na baya-bayan nan da suka buga a gasar UEFA, amma kwazon da Roma ta yi a baya-bayan nan a Turai ya nuna cewa kulob din na Italiya ya shirya tsaf don wannan karawar da za ta iya kai ta zagayen 16.
- Ko Barcelona Za Ta Iya Sake Zazzagawa Valencia Ƙwallaye 7 Yau?
- Arsenal Ta Fice Daga Gasar EFL Bayan Shan Kashi A Hannun Newcastle
Roma wadda ta lashe gasar Europa League a 2022, sun kai matakin wasan ƙarshe da na kusa da na karshe na gasar UEFA Conference League a shekaru biyu a jere, Roma na matsayi na tara a gasar Seria A bayan wasan da suka doke Venezia da ci 1-0 a ranar Lahadi sannan kuma an fitar da ita daga gasar Copa Italia.
Yan wasa 11 na farko da FC Porto za ta yi zubi dasu:
Kosta, Djalo, Perez, Otavio, Mario, Eustaquio, Varela, Moura, Pepe, Mora, Aghehowa
Yan wasa 11 na farko da Fc Porto za ta yi zubi dasu:
Svilar, Mancini, Hummels, Ndika, Saelemaekers, Kone, Paredes, Angelino, Dybala, Pisilli, Dovbyk