Kasashen yankin Afirka ta yamma uku, Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sanar da ficewar su daga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.
Kasashen sun bayyana cewa matakin nasu zai fara aiki ne nan take.
- Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A KuÉ—in Naira
- Me Ya Sa Kamfanonin Jamus Fiye Da 560 Suka Zabi Wani Gari A Kasar Sin Don Gudanar Da Harkokinsu?
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, shugabannin sun zargi kotun da zamewa “‘‘yar koren masu mulkin mallaka” wadda take “nuna son zuciya wajen yin hukunci.”
Sanarwar wadda shugabannin kasashen suka fitar ta kuma zargi Kotun Hukunta Manyan Laifukan ta duniya da hukunta mutane daga kasashe marasa karfi, kuma ta nuna cewa “ta gaza” wajen hukunta laufuka mafi muni da ake tafkawa a doron kasa.
Wannan dai daya ne daga cikin matakan da kasashen uku suka dauka a baya-bayan nan bayan ficewarsu daga kungiyar hadin kan yammacin Afirka ta Ecowas, da kuma kafa kungiyar kasashen Sahle, wato AES.
A shekarar 2003 ne aka kafa kotun ta ICC wadda aka dorawa alhakin hukunta laifukan da suka shafi kisan kare dangi da cin zarafin bil’Adama da laifukan yaki kuma tun lokacin da fara aiki kotun ta ICC ta saurari kararraki 33
Masu sukar kotun ciki har da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame sun zargi kotun da nuna son zuciya ko rashin adalci saboda ta fai maida hanakli kan kasashen Afrika. Sai dai magoya bayan kotun sun ce rashin tasirin fannin shariar kasashen Afrika ne ya sa mutane ko gwamnatoci ke neman adalci a kotun ta ICC
kasashen yannkin Sahel uku wadanda a halin yanzu ke fama da rashin tsaro sakamakon hare-haren mayaka masu ikirarnin jihadi sun yanke alaka da wasu kasashen yamma da suka hada Faransa inda suka kulla kawance da Rasha domin samun tallafin soji da kuma inganta cinikayya tsakaninsu.
Kasashen 33 daga cikin 54 mambobi ne a kotun ta ICC kuma ta ta fara bincike a wasu kasashen Afrika da suka gada jamhuriyat tsakiyar afrika da jamhuriyar dimokradiyar Kongo da Kenya da Libya da kuma Mali sauran sun hada da Sudan da Uganda da kuma Iboyry cost Yarjebiyar kafa Yarjejeniyar da ta kafa kotun ta bai wa mambobinta damar janyewa, sai dai matakin zai fara aiki ne bayan shekara guda daga lokacin sanarwar.
A shekarar 2017, Burundi ta zama kasa ta farko kuma daya tilo daga Afirka da ta yi nasarar ficewa daga kotun ta ICC.
Mece ce kotun hukunta manyan laifuka, kuma mene ne aikinta?
Babban aikin kotun hukunta manayan laifuka shi ne gurfanarwa da kuma hukunta mutanen da ake zargi da aikata kisan kiyashi, da laifukan yaki da kuma sauran laifuakan cin zarafin bil’adama.
Haka nan kotun takan iya yin bincike tare da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata munanan laifuka da suka zamo abin damuwa tsakanin kasashen duniya.
Kotun takan kuma fafutikar da duniya ke yi na yaki da cin zarafi ta hanyar tabbatar da adalci.
Makasudin kafa kotun shi ne domin a tuhumi masu irin wannan laifuka da nufin zamewa darasi ga na baya ta yadda za a kauce wa faruwar irin wadannan laifuka.
Kotun ita ce mataki na karshe da za a iya bi, kuma ba an yi ta ne domin maye gurbin kotuna na cikin gida ba, sai dai domin ta taimaka musu.
An samar da kotun ne daga yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen duniya, wadda ake kira ‘Rome Statute.
Ita ce kotu ta farko ta duniya da aka kirkira domin hukunta manyan laifuka.
Kotun ICC na son ganin kasashe su amince da ita, domin samun karfin yaki da cin zarafi da kuma kare faruwar hakan a gaba.
Yanzu haka kotun tana da ma’aikata sama da 900 daga kimanin kasashe 100 na duniya.
Kotun na amfani da harsuna shida a hukumance, wato Ingilishi da Faransanci da Larabci da yaren China da na Rasha da kuma Sifaniyanci.
Kotun ta ce ta bayar da sammacin kame 61 ta hanayar hadin kai da kasashen duniya, kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.
Haka nan ta samu nasarar tsare mutane 22 wadanda ta gurfanar a gabanta.
Har yanzu akwai mutane 30 wadanda ba ta samu damar kamawa ba, inda ta yi watsi da tuhume-tuhume kan mutum 8 sanadiyyar mutuwa.
Daga shekara ta 2002, alkalan kotun sun bayar da sammacin kama mutum tara domin gurfana a gabansu.
Haka nan sun samu nasarar kama mutum 11 da laifi yayin da suka wanke mutum 4.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp