Shugaba Bladimir Putin ya lashe zabe karo na biyar, inda zai ci gaba da jagoranci har shekara ta 2030.
A jawabin da ya yi bayan samun nasara, ya ce nasararsa za ta sanya Rasha ta kara samun karfi da kuma yin tasiri.
- Noman Gwanda Da Kasuwancinta A Saukake
- Ku Yi Amanna Da Tinubu, Matsalolin Zu Su Zo Karshe, inji Ministan YaÉ—a Labarai
Ya lashe zaben ne da gagarumar nasara inda ya samu kashi 87 na kuri’un da aka kada, abin da ya zarce wanda ya samu a zaben da ya gabata na kashi 76.7 na kuri’un. Duk da cewa bai samu wata adawa mai karfi ba, fadar Kremlin ita ke iko da tsarin siyasar kasar, da kafafen yada labaru da kuma zabuka.
Shugabannin kasashen Yamma da dama sun yi Alla-wadai da zaben inda suka ayyana shi a matsayin mai rashin inganci, ciki har da shugaban kasar Ukraine Bolodymyr Zelensky, wanda ya kira Putin a matsayin mai mulkin kama karya wanda kuma giyar mulki ta buga, inda ya kara da cewa: “Zai iya yin komai domin ci gaba da zama a kan mulki.”
Putin, mai shekara 71, wanda ya fara shugabanci a ranar karshe ta shekarar 1999 – ya kasance shugaban kasar mafi dadewa kan mulki tun bayan Joseph Stalin, kuma a halin yanzu zai karya tarihin da mutumin mai mulkin kama-karya na tarayyar Sobiet ya kafa a baya.
Duk da cewa ‘yan Rasha na mutuwa a yakin da take yi da Ukraine, wanda ke shiga shekara ta uku da farawa, yayin kuma da Rasha take kara zama saniyar ware tsakanin kasashen Yamma, ga wasu dalilai da suka sa Putin ya ke da karfin iko da ba a taba gani a baya ba.
Girman tattalin arzikin Rasha
Duk da irin tarin takunkumi da aka kakaba wa Rasha bayan mamayar da ta yi a Ukraine, kasar ta bai wa masana tattalin arziki da dama mamaki ta hanyar zama kasar da tattalin arzikinta ke habaka cikin sauri a Turai.
“Tattalin arzikin na cikin yanayi mai kyau, dukkan abubuwa na tafiya yadda ya kamata, kuma hakan ya saka Putin zama sananne saboda ya sake nuna kansa a matsayin mutumin da ya bijire wa Yamma kan takunkumi da suka saka wa tattalin arzikin Rasha,” in ji wakilin BBC a bangaren kasuwanci, Aledey Kalmykob.
Maimakon faduwa kasa kamar yadda mutane da dama suka yi tsammani, tattalin arzikin Rasha ya karu da kashi 2.6, a cewar kiyasin Hukumar Ba Da Lamuni ta Duniya (IMF), duk da takunkuman Yamma, da suka hada da hana Rashar taba kudinta da ya kai Dala biliyan 300.
Sai dai wadannan takunkumai ba su yi aiki a fadin duniya ba. Wannan ya bai wa Rasha damar huldar kasuwanci da kasashen China, Indiya da kuma Brazil yayin da makwabta, ciki har da Kazakhstan da Armenia, na taimaka wa Rasha kauce wa takunkuman Yamma.
“Tattalin arzikin Rasha na da grima,” in ji Kalmykob, ya kara da cewa: “Za a dauki tsawon gomman shekaru kafin takunkumai ko barnar kudi su kai tattalin arzikin Rasha kasa kasa amma dai ba yanzu ba.”
“Rasha na samun kudi ta hanyar fitar da kayyaki waje kuma tana da damar sayar da duk abin da take so,” a cewar Kalmykob. “takunkumi kan man fetur na je ka na yi ka ne, sai dai babu takunkumi kan iskar gas da kuma nukiliya daga Tarayyar Turai saboda suna cikin wadanda ke sayen abubuwan daga Rasha.”
Dakta Schulmann ya ce duk da cewa farashin kayyaki ya ninka har sau hudu ba kamar a baya ba, a shirye suke, wanda ta ce yana da muhimmancin gaske.
“An san Rasha da kara farashin kayayyaki. Fargabar da muke da ita ba wai ta hauhawar farashi ba ne, sai dai illa gibi.
Kalmykob ya amince cewa: “Abu daya shi ne farfagandar Putin na iya yin tasiri matuka.”