Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwarsa kan gazawar Nijeriya wajen cimma wadatar abinci duk da yalwar albarkatun da take da su. Ya ce abin kunya ne a ce ƙasa mai yawan jama’a miliyan 250 har yanzu ba ta iya ciyar da ‘yan ƙasarta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar bakuncin jakadan Portugal a Nijeriya, Paulo Martins Santos, a fadar gwamnatin Bauchi. Ya jaddada cewa Bauchi na da filayen noma masu girman hekta miliyan huɗu, kuma gwamnatinsa za ta samar da yanayi mai sauƙi ga masu zuba jari daga Portugal ba tare da matsalolin cin hanci ko haraji mai yawa ba.
- Adadin Sana’o’in Adana Kayayyaki Na Sin Ya Karu Da Kashi 52.5%
- Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Mashawarta 11, Ya Horesu Da Aiki Tuƙuru
Bala Mohammed ya kuma yi bayani kan albarkatun ƙasa da Bauchi ke da su, irin su zinariya, ƙarfe, tantalite, da duwatsu masu daraja. Ya tuno da tsohuwar dangantaka tsakanin Nijeriya da Portugal tun daga ƙarni na 15, yana mai yabawa ƙasar Portugal kan kyakkyawar hulɗarta da Nijeriya.
A nasa jawabin, Jakada Paulo ya jaddada muhimmancin sabunta dangantakar kasuwanci da ci gaba da haɓaka haɗin gwuiwa tsakanin ƙasashen biyu. Ya kuma bayyana cewa kamfanin Portugal mafi girma a Nijeriya yana aikin gina layin dogo daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar, wanda ke nuna ƙarin shigar Portugal cikin ci gaban Nijeriya.