Kwanan baya, wakilin kasar Sin ya bayyana matukar damuwa a yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 51 dangane da yadda hukumomi masu ruwa da tsaki na kasar Amurka da wasu kasashe suke nuna wa ‘yan kananan kabilu bambanci yayin da suke aiwatar da doka, ya kuma bukace su da kalli kansu yadda ya kamata dangane da mummunar matsalar wariyar launin fata da nuna bambanci tsakanin kabilu, su aiwatar da sanarwa da tsarin ayyuka na Durban, a kokarin kaucewa sake abkuwar abin tausayi da ya wakana kan George Floyd.
Shekara guda bayan mutuwar George Floyd, ‘yan sandan Amurka sun kashe ‘yan asalin Afirka a kalla 229, lamarin da ya sake bayyana rashin gaskiyar Amurka ta fannin kare hakkin dan Adam. Amurka, kasa ce da ba a tabbatar da babban hakkin dan Adam na rayuwa, kuma babu demokuradiyya ko kadan.
A watan Agustan bana, kwamitin yaki da wariyar launin fata na MDD ya soki Amurka kan batun nuna wariyar launin fata da ya dade yana addabar Amurka, yayin da yake duba yadda Amurka take aiwatar da yarjejeniya mai ruwa da tsaki.
Kana kuma, a yayin taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 51 da ake gudanarwa, mahalarta taron sun bukaci Amurka da ta dauki tsauraran matakai don kawar da wariyar launin fata a kasar baki daya.
Bai kamata Amurka ta kau da kai daga sukan da kasashen duniya ke yi mata ba. Ya dace ta saurari wannan batu da idon basira, ta fara kyautata halin da ake ciki a cikin gidanta a fannin kiyaye hakkin dan Adam, ta duba ta kuma yi gyara kan dokoki, manufofi da matakai masu nasaba da wariyar launin fata a cikin gida, ta bi bahasin batutuwan cin zarafi da ‘yan sandan kasar suka aikata, ta aiwatar da doka kan masu cin zarafin da kuma biyan diyya ga wadanda aka ci zarafin nasu. (Tasallah Yuan)