Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto,
Alhaji Mukhtar Shagari, ya bayyana cewa, an tuntube shi kan ya amince ya yi wa dan takarar shugaban kasa a jamiyyar LP, Peter Obi Mataimaki amma ya ki karbar tayin.
Shagari wanda ya sanar da hakan a hirarsa da gidan talabin na Channels ya ce, a matsayinsa na jigo a jam’iyyar PDP ya ce, yana da yakinin jam’iyyar LP ba za ta yi nasara a kan PDP a zaben 2023 ba, inda ya buga missali da cewa, Jam’iyyar LP a jihar Sokoto babu ita.
Ya ce, an tuntube ni yiwa Obi Mataimaki, amma ba zan iya rabuwa da PDP ba domin na aminta da manufofin ta, inda ya kara da cewa, shin a jihar Sokoto wanene shugaban LP, su waye ‘yan takarar, wa ke takarar gwamna, wa ke takarar Sanata, inda ya ce, har yau ban samu amsohin wadannan tambayoyin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp