Tsohon Shugaban Nijeriya a mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya amince da cewa marigayi Shugaba Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya lashe zaɓen shugaban kasa na na 12 ga watan Yunin 1993, da gwamnatinsa ta gudanar.
Wannan furuci na Janar Babangida, yana ƙunshe ne cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “A Journey In Service”, wanda aka ƙaddamar yau Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.
- Hisbah Ta Haramta Gidajen Casun Dare A Katsina
- Wang Yi Ya Bayyana Ra’ayin Sin Kan Yadda Za A Karfafa Huldar Cude-Ni-In-Cude-Ka A Duniya
A yayin da yake bayani kan littafin, a matsayin wanda ya nazarta, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Janar Babangida, ya tabbatar da cewa marigayi MKO Abiola, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar SDP, da ta ta wancan lokacin ya samu rinjayen ƙuri’u mafi yawa da za kai shi zama shugaban ƙasa.
Osinbajo ya ce marubucin littafin ya bayyana soke zaben Yuni 12 a matsayin abu mafi wahalar da ya yi a rayuwarsa, amma yana farin cikin cewa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, daga baya ya amince da cewa Abiola ne ya lashe zaɓen, sannan ya karrama shi da babbar lambar girma ta ƙasa, wato (GCFR), wadda aka tanadar domin shugabannin ƙasa.
Taron ƙaddamar da littafin, wanda ake gudanarwa a Transcorp Hilton Hotel da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya samu mahalartar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da tsofaffin Shugabannin Ƙasa da suka haɗa da Janar Yakubu Gowon, da Janar Abdulsalami Abubakar, da tsofaffin Mataimakan Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da Namadi Sambo da sauransu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp