Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki kafin amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
Bayan taron majalisar zartarwa, ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya bayyana cewa, duk da an miƙa rahoton kwamitin ɓangarori uku ga shugaban ƙasa, matsalar ta na buƙatar ƙarin tattaunawa.
- Rayuwar ‘Yan Jari-bola Bayan Fatattakar Su A Abuja
- Za Mu Canza Salon Yaƙin Da Muke Yi Da Ƴan Bindiga a Nijeriya – Bola Tunibu
Idris ya bayyana cewa sabon mafi ƙarancin albashin ba kawai ya shafi gwamnatin tarayya ba ne, har ma da jihohi da ƙungiyoyin masu zaman kansu. Don haka, Shugaba Tinubu ya nemi duk masu ruwa da tsaki don yanke shawara mai kyau.
Majalisar zartarwa (FEC) ta tattauna kan lamarin amma ta yanke shawarar jinkirta yanke hukunci nan take don ba da damar samun cikakkun bayanai daga dukkan bangarorin da abin ya shafa.