Tsohon kakakin shugaban ƙasa Laolu Akande ya bayyana cewa ana yawan aikata wasu abubuwa da sunan Shugaba Bola Tinubu ba tare da amincewarsa ba. A wata hira da ya yi a shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin ɗin Channels, Akande wanda ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, ya bayyana yadda wasu shawarwari a Aso Rock kan fita ba tare da sanin shugaban ba.
“Ana yawan yin abubuwa da yawa a sunan shugaban kasa wanda mai yiwuwa ba shi ne ya qaddamar da su ba,” in ji shi, yana ƙara da cewa Tinubu na iya yin watsi da su ko kuma ya soke idan bai yarda da su ba.
Maganganun Akande sun zo ne a lokacin da jama’a ke nuna rashin amincewa da naɗin wasu masu gudanarwa na gundumomi a jihar Rivers da tsohon kwamandan Sojojin ruwa Ibok-Ete Ibas ya yi.
Yayin da wasu ‘yan Nijeriya ke nuna shakku kan halaccin wannan matakin, Akande ya nuna cewa shirun shugaban ƙasa ba zai nuna amincewa ba, yana mai cewa shugaban yana hutu a Faransa a lokacin. “Wasu daga cikin abokansa sun shawo kansa kada ya ɗauki wannan matakin,” in ji shi, yana nuna cewa akwai rashin jituwa a cikin gwamnati.
Dangane da kwatankwacin ayyukan Tinubu da na tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a jihohin Plateau da Ekiti, Akande ya yi gargadin cewa bai kamata a rage matsayin gwamnati ba. “Tinubu da Obasanjo suna da tarihin siyasa daban-daban,” in ji shi.
“Zai kasance abin takaici idan Tinubu ya maimaita irin waɗannan ayyuka ko ya aiki mafi muni.”
Maganganun nasa suna nuna rashin jituwa tsakanin fadar shugaban ƙasa da kuma karya dokokin cikin hukumomin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp