Har yanzu ana ci gaba da jimami tare da tafka muhawara a kan kisan gillar da aka yi wa matafiya mafarauta ‘yan Arewacin Nijeriya a garin Uromi da ke Jihar Edo a kudancin kasar, lamarin da ya ja hankalin al’ummar kasar baki-daya.
Mutane da dama daga wannan yanki na arewa, sun yi Allah wadai tare da yin kira da a dauki matakan gaggawa ta hanyar yin bincike da hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika, don kiyaye sake afkuwar hakan a nan gaba.
- Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
- Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi
Wadannan matafiya mafarauta dai, suna kan hanyarsu ne daga garin Fatakwal na Jihar Ribas zuwa Kano, domin gudanar da bukukuwan sallah, sai wasu ‘yan banga suka tare su bisa zargin cewa; masu yin garkuwa da mutane ne.
Har ila yau, wadanda wannan iftila’i ya shafa din; ‘yan asalin Jihar Kano ne daga kauyen Torankawa da ke karamar Hukumar Bunkure, sauran kuma sun fito ne daga kauyukan Garko, Kibiya da kuma Rano.
kauyen Torankawa, wanda aka jefa cikin wannan jimami na zaman makoki tun bayan faruwar al’amarin, ya shahara wajen farautar balaguron mafarauta, wanda a halin yanzu ake kallon al’amarin a matsayin wata jarrabawa da ta samu wadannan da suka yi shahada.
Shida daga cikin wadanda aka kashe da kuma guda daya da ya tsira, sun fito ne daga kauyen. Daga cikin wadanda suka rasu akwai Abdulkadir Umar, ya bar mata biyu da mahaifiyarsa; Zaharaddeen Tanko, ya bar mata daya da ‘ya’ya hudu, sai kuma Haruna Hamidan, wanda shi ma ya bar mata da ‘ya’ya hudu.
Sauran su ne, Usaini Musa, wanda ya bar mata biyu da ‘ya’ya biyu; Abdullahi Harisu, wanda ya yi aure wata hudu da suka gabata; sai kuma Ya’u Umaru da kuma Abubukar Ado, wadanda dukkaninsu samari ne.
Shugaban mafarautan, Ibrahim Isa, mai ‘ya’ya shida; wanda shi kadai ne ya tsira daga kauyen, yana kwance a wani asibiti da ke Jihar Edo.
Muhammad Sunusi Torankawa, kanin shugaban mafarautan da ya tsallake rijiya da baya, ya tuno hirar da suka yi ta wayar tarho da shi a daidai lokacin harin.
“Ya kira ni cikin dimuwa yana cewa, suna cikin hadari kwarai da gaske, don haka mu sanya su cikin addu’a. Kana ya ce da ni, an kai masa hari da adduna a kafadarsa, kusa da wuyansa, amma cikin ikon Allah ya samu ya tsira, sakamakon dafa’in da yake tare da shi.
“Ya ba ni labarin yadda ya buya, yana ganin yadda ake jan mutanensa daya bayan daya, ana cinna musu wuta, wanda hakan ya sa ya ji kawai shima ya saduda, domin kuwa zai iya mutuwa ta hanyar jinin da ke zuba a jikinsa.
“Amma cikin ikon Allah, jami’an tsaro suka ceto shi tare kuma da kai shi asibiti, yanzu haka yana can ana kokarin ceto tasa rayuwar”, in ji shi.
Na Rasa da Da kani Da dan ‘Yar’uwata
Wata mata, mai suna Sadiya Sa’adu, ta bayyana cewa; baya ga dan cikinta da ta rasa mai suna Haruna Hamidan, ta kuma rasa dan’uwa da dan ‘yar’uwarta a wannan harin.
Sannan, ta yi kira ga hukuma wajen tabbatar da ganin an yi adalci, ta hanyar bi musu hakkinsu na wadanda suka rasa.
Ta ce, “Ba masu laifi ba ne, kawai suna zuwa wannan farauta ne, domin rufawa kawunansu asiri. Don haka, jinin dana ba zai tafi a banza ba.
“A matsayina na uwa, na yafe masa, ina kuma rokon Allah ya gafarta masa, musamman ganin ga shi ya rasu a cikin wata mai daraja na Ramadana. Saboda haka, ya zama wajibi hukuma ta yi bincike a kan wannan al’amari da ya faru tare da hukunta dukkanin wadanda aka samu da hannu a ciki.
“Wannan abu ne da suka jima suna yi, ba yanzu suka fara ba, suna neman yadda za su ciyar da kawunansu ne da kuma iyalansu, sannan kuma ba barayi ba ne, ba kuma ‘yan ta’adda ba.
“Kazalika, ba shi kadai na rasa ba, akwai dan ‘yar’uwata da kuma dan’uwana, wanda dukkaninmu dangi daya ne.”
‘Maganata Ta karshe Da dana’
Aisha Harisu, mahaifiyar daya daga cikin mafarautan da aka kashe, Abdullahi Harisu, dan shekara 21 ta ce; danta wanda ya yi aure wata hudu da suka wuce, ta tuna tattaunawar da ta yi da shi ta wayar tarho.
Ta ce, “Ya kira ni, yake cewa da ni; Umma, don Allah ki yi mana addu’a.” Wannan ita ce maganata ta karshe da shi. Shi ne wanda yake daukar dukkanin dawainiyarmu ta rayuwa.”
Kwamandan ‘Yan Banga Na Edo Ne Ya Ba Da Umarnin Kisan- Direban Motar
Direban mafarautan da aka kashe ya ce, Kwamandan kungiyar ‘Yan Banga a jihar, shi ne ya bayar da umarnin a kashe su.
A wani faifan bidiyo, direban ya bayyana yadda aka kai wa mafarautan hari. “Na dauko wasu kaya daga kamfaninmu da ke Obajana, da na isa Illele, sai na ga wadannan mutane, ‘yan’uwa nawa daga arewa, wadanda mafarauta ne daga karamar Hukumar Rano, suna kan hanyarsu ta zuwa gida, domin gudanar da bikin sallah, sai na fada musu cewa; tsarin kamfaninmu ya haramta mana daukar fasinjoji, amma tunda ku ‘yan’uwana ne, zan dauke ku.
Da farko, har na bar su na yi tafiya ta kusan kilo mita biyu, kafin na tsaya na sake yin tunani cewa; na yasar da ‘yan’uwana da ke makale a kudu suna neman taimako, daga nan ne, kawai sai na juya na koma wurinsu. Lokacin da na ce da su, ba zan iya barin su ba, sun yi mamaki kwarai tare da matukar jin dadi.
“Ba mu samu wata matsala ba, har sai da muka iso Uromi, inda aka tsayar da mu. A nan ne, suka tambayi kayan da nake dauke da su, na nuna musu takardar kudin kayana, sannan sai suka tambayi mutanen da nake tare da su, na fada musu ko su wane ne, amma shugabansu ya ki amincewa da ni. Daga nan ne, sai daya daga cikinsu ya hau motar, sai ya ga bindigogin farauta da karnukansu, nan take ya bayyana cewa; wadannan mutanen ‘yan Boko Haram ne, kuma masu garkuwa da mutane.
“Ba tare da wani bata lokaci ba, suka fara fasa gilashin motata tare da fara dukanmu da jifanmu. Daga nan ne kuma, sai kwamandan ‘yan bangar, ya daure ni tare da wani dattijo mai suna Haruna da kuma wani matashi mai suna Ila, suka ci gaba da dukan sauran.
“Nan ne fa, aka kai mu caji ofis na ‘yansanda, inda kwamandan ya shaida wa jami’an cewa; ya kawo musu masu garkuwa da mutane. Haka nan, aka kulle mu, amma kafin ya bar wajen, tuni ya bayar da umarnin kashe sauran. Hakan kuma aka yi, inda aka yi wa mutum 16 ko 17 kisan gilla.
“Game da ikirarin gwamnan na cewa, wannan ba rikicin kabilanci ba ne, karya yake yi! Ni da mafarauta ne kadai, ‘yan banga suka tare, suka kuma yi wa ‘yan’uwanmu mummunan kisa.”
Yadda Muka Ceto Mafarauta Goma Daga Kisa
Kakakin Rundunar ‘Yansandan Jihar, Moses Yamu, ya bayyana cewa; da jin harin, jami’an rundunar suka garzaya inda al’amarin ya faru tare da ceto mutum 10 daga cikin matafiyan da harin ya rutsa da su tare kuma da garzayawa da su zuwa asibiti, domin yi musu magani.
Gwamnan Edo Ya Kai Ziyarar Jaje Kano
Gwamnan Jihar Edo, ya kai ziyarar jaje ga Gwamnan Kano da kuma iyalan mafarauta 16 da aka yi wa kisan gilla ta hanyar kone su kurmus a garin Uromi da ke Jihar Edo, lamarin da ya harfar da cece-kuce a fadin kasar, musamman a yankunan arewa, ta hanyar yin Allah wadai da kuma bukatar yi wa mamatan adalci.
Da yake jawabi a gidan Gwamnatin Kano, Gwamna Okpebholo, ya nuna matukar kaduwarsa da afkuwar wannan lamari, inda ya bayyana cewa; mutane 14 daga cikin wadanda ake zargi da aikata kisan, sun shiga hannu tare da bayar da tabbacin cewa; gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen tabbatar da adalci ga iyalan mamatan.
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusif, ya bukaci Gwamnan Edon, ya tabbatar an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika, ya kara da cewa; dole ne a bi doka da oda, domin tabbatar da ganin hakan bai sake faruwa a nan gaba ba, a ko’ina a fadin wannan kasa.
Gwamna Yusif, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bayyana sunaye da fuskokin mutanen da aka kama dangane da kisan gillar, wanda a cewarsa hakan zai hana sake afkuwar irin wannan danyen aiki a nan gaba.
Daga karshe, Gwamnan Kano, ya bukaci Gwamnatin Jihar Edo, da ta tabbatar an biya diyya ga iyalan mamatan, domin rage musu radadin wannan mummunan al’amari da ya same su.
Kamar yadda Gwamnan Jihar Edon ya bayyana kama mutum 14 da ake zargi da aikata wannan ta’asa, jami’an ‘yansanda su ma bayyana cewa; an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan wadannan mafarauta 16 ‘yan arewa a Jihar Edo.
Kakakin ‘yansanda na Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa wannan labari a shafinsa na sada zumunta (facebook).
Kazalika, ya bayyana cewa; za kuma za a mika su ofishin DIG Sadik Abubakar, mni (Dan Asalin Jihar Kano), kuma DIG da ke wakiltar Arewa Maso Yamma, sannan kuma mai kula da sashen binciken manyan laifuka, domin gudanar da bincike da kuma gurfanarwa a gaban Kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp