Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Talata 21 ga wata cewa, abubuwan da suka shafi kasar Sin a cikin “Rahoton Kare Hakkin Dan Adam na Kasashe Daban Daban na Shekarar 2022” da Amurka ta kaddamar, cike suke da karairayin siyasa da raini, kuma irin maganganun da ke cikin rahoton a kowace shekara ba su cancanci a saurare su ba.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da “Rahoton Kare Hakkin Dan Adam na Kasashe Daban daban na Shekarar 2022” a ranar 20 ga watan nan na Maris, kuma Antony Blinken ya yi jawabi kan hakan, inda ya sake nuna yatsa kan halin kare hakkin dan Adam da kasar Sin ke ciki. Dangane da haka, Wang Wenbin ya ce, abin da duniya ke gani daga rahotannin kare hakkin bil’adam da Amurka ke fitarwa kowace shekara, ba wai batun kare hakkin bil’adama ne na kasashe daban daban ba, a’a, girman kai da cin zarafi da Amurka ke yi ne, da kuma ma’auni biyu da take dauka kan ita kanta da sauran kasashe.
Dangane da tambayar da dan jarida ya yi game da sanya hannu da shugaban Amurka Joe Biden ya yi kan kudurin “Shirin Dokar Asalin COVID-19” don ya zama doka kuwa, Wang Wenbin ya ce, abubuwan da ke da alaka da kasar Sin dake cikin shirin dokar ta Amurka, suna murguda gaskiya, kuma suna tattara bayanan karya, da kuma bata sunan kasar Sin. Kasar Sin na nuna rashin jin dadi kan hakan, kuma tana adawa da hakan. A cewar kakakin, a ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen gano asalin yaduwar COVID-19, wato tana goyon baya da kuma shiga cikin ayyukan duniya, na gano asalin cutar ta hanyar kimiyya, yayin da take adawa da duk wani nau’i na magudin siyasa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)