Zama a kasa cikin tayis ko siminti, sannan da A.C ba wando.
Uwargida kar ki kasance kina zama a kasa cikin sanyi yin hakan yana kawo miki matsalar kamuwa da tusar ko kuma sanyi wanda wadannan cututtuka ne da suke da wahalar magani ga mace, sannan kuma suna kawo mata cikas a rayuwar aurenta.
Uwargida ki kasamce mai kamewa, sannan kuma ma gyara, kar ki zama babu wando ko babu siket duk ba naki bane saboda su kansu akwai nasu taimakon da suke yi suna kare miki duk wani abubuwa da zai shiga datti ne ko tafiya kike suna kare ki daga korar da take tashi ba za ta shiga jikinki ba, sannan ke kanki za ki fi jin dadin kanki idan ki ka sa su ba za ki rika jinki kamar kina tafiya tsirara ba.
Yawo ba takalmi musamman ma a AC kuma a kan tayis:
Yawo babu takalmi yana kawo tusar gaba ko kuma kamuwa da sanyi, Uwargida ki kasance kina da takalmin yawo a cikin gidanki za ki samu takalmin wanda ba kya fita da shi ko kuma ki saya musamman saboda yawo a cikin gidanki saboda martabar jikinki.
Kar ki rika kwanciya ki kunna fanka kuma ba wando a jikinki:
Da yawa wasu matan sai ki ji suna cewa wai iska suke sha sai su zage su kunna fanka sannan kuma su wage kafafuwa wai saboda su sha iska, to iskar fankar nan ita ce idan ta shiga sai ki ga mace ta fara tusar gaba, iska ba, a ce kar ki sha iska ba amma kar ki kunnan fanka ko AC sannan kuma kar ki kware kafafuwa.
Rashin yin tsarki da ruwan zafi:
Rashin yin tsarki da ruwan dumi yana haifar da tusar gaba ba wai lalla sai ruwan zafi ba mai dan dumi haka idan ke ba ma’abociyar san ruwan zafi bace yadda za ki kashe sanyin ruwan, tsarki da ruwan dumi yana da kyau sosai.