• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Shugaban Kasa Ya Wajabta Min Yi – Ministan Yada Labarai

by Sulaiman
2 years ago
Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce, Shugaba Tinubu ya ɗora masa nauyin jaddada tasirin kishin ƙasa, aiki da gaskiya da kuma kawar da nuƙu-nuƙu, a matsayin kyawawan ɗabi’un da gwamnatinsa za ta ɗore kan turbar su.

Ministan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a Abuja.

  • Ministan Wutar Lantarki Ya Lashi Takobin Samar Da Megawat 20,000 Na Wutar Lantarki A Nijeriya
  • Minista Ya Nemi Google Ta Dakatar Da Yada Labarai Masu Barazana Ga Hadin Kan Nijeriya

Ya ce, ajandar Fata Nagari Lamiri da gwamnatin Shugaba Tinubu ta hau mulki da ita, wani kyakkyawan muradi ne na ɗaukaka Nijeriya zuwa ƙololuwar nasara da bunƙasa a cikin manyan ƙasashe na duniya, tare da shafe baƙin fentin da ake kallo a jikin wannan ƙasar.

Idris ya ce, Tinubu ya hore ni da kafuwa wurin ganin mun samu nasarar wayar da kan ‘yan Nijeriya cikin shekaru kaɗan masu zuwa, ta yadda aƙalla za mu iya sake kankaro ƙima da martabar ƙasar nan, tare da fara ɗorawa bisa kyakkyawar turbar da ta fi dacewa mu bi.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

“Wannan kuwa babban kalubale ne. Saboda kun dai san ba a zukatan matasa kaɗai ɗa’a da kishi su ka yi ƙaranci ba, har ma a zukatan yara da manya.

“Ina ganin dalili kenan da ya sanya shugaba Tinubu  ya canja sunan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Bunƙasa Al’adu, zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

“Hakan, ya na nufin shugaban ƙasa na so ɗora batun wayar da kai da cusa kishin ƙasa a sahun gaba,” cewar Idris.

Ministan ya ƙara da cewa, tasirin kishin ƙasa da aiki da gaskiya, Tinubu ke ta faɗi-tashin cusawa da kwaɗaitarwa.

“Ya ba mu umarni kai-tsaye cewa, mu tabbatar waɗannan kyawawan ɗabi’u da halaye nagari sun kasance jigo a ƙoƙarin faɗakar da mafi yawancin ‘yan Nijeriya.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima
Manyan Labarai

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Next Post
Layin dogo

Kasar Sin Za Ta Kammala Aikin Layin Dogo Daga Abuja Zuwa Kano Da Fatakwal Zuwa Maiduguri

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.