A likitance ana kiran Dannau da (sleep paralysis), a gargajiyance kuma ana kiran sa da Aljanin dare. A nan wani yanayi da mutum yake samun kansa a yayin bacci ko a farke, ta hanyar da mutum yana ji yana gani ya kasa yin numfashi ko motsi. A irin wannan lokaci, wasu har gane-gane suke yi barkatai; shi ya sa ake alakanta al’amarin da shedanu ko Mayu da sauran makamantansu.
Bugu da kari, duk a cikin mutum goma; akalla ana samun mutum hudu da ke shiga cikin irin wannan yanayi lokaci zuwa lokaci, sannan duk wanda ya samu kansa a wannan yanayi, ba ya wuce wasu ‘yan dakiku ko mintuna kafin ya samu kansa ko ya dawo hayyacinsa.
- Hisbah Ta Yi Wa Mutum 4,000 Rajista Da Ke Son Gwamnatin Kano Ta Aurar Da Su
- Duk Da Hukuncin Kotu, Gwamna Yusuf Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 3 Kan Ayyuka
Har ila yau, wannan yanayi da yake da alaka da Dannau, kamar yadda likitoci suka bayyana, yana faruwa ne sakamakon yadda baccin kowane Dan Adam ya rabu zuwa gida biyu, wanda a turance ake kira da ‘REM sleep’ da kuma ‘Non REM sleep’, ma’ana matakin bacci na farko da kuma na biyu. A matakin farko ne mutum yake samun damar yin mafarki, a inda kwakwalwa ke aike wa da gabobin Dan Adam da sako ta yadda idan yana yin bacci zai iya motsawa duk inda yake so a kuma duk lokacin da ya gama.
Saboda haka, a wannan lokaci na matakin bacci na farko (REM sleep), kwakwalwar na kashe mukunnin da ke kai wannan sako zuwa gabban mutum don gudun ka da ya yi hanzari ko gaggawar tashi ta kai shi ga jin ciwo ko rauni. Don haka, idan mutum ya zo tashi daga bacci, ya kamata kwakwalwar tasa ta gane cewa ya zo tashi, ta koma ta sake kunna makunnin wadannan gabbai nasa kafin ya kai ga tashin, amma a wasu lokutan sai a samu akasin haka kwakwalwar ta ki kunna wannan makunni, daga nan sai a samu akasi mutum ya kasa motsi ko yin numfashi har zuwa wasu dakikai ko ‘yan mintina kafin kwakwalwar ta gano cewa ta yi kuskure ba ta kunna ba, ta dawo ta sake kunna wannan mukunni.
Haka nan, a gargajiyance ana alakanta wannan matsala ta Dannau da Aljanin dare ko sharrin Mayu. Duk da cewa, yanayin da ake shiga kamar yadda a likitance aka bayyana iri daya ne, ta yadda mutum zai ji ya kasa numfashi ko motsi har zuwa wasu ‘yan dakikai ko mintina. Sannan, sau tari mutum ya kan ji jikinsa ya yi nauyi kamar an dora masa wani katon dutse ko an daddaure shi takamau; a cikin baccinsa ko ido biyu, wani lokacin ma wasu kan ce har shedanun ake gani ido kuru-kuru.
Wasu kuma na danganta wannan al’amari kai tsaye ga matsalar Mayu, ta yadda a cewarsu; ana ganin Mayen a daidai wannan lokaci, ko ya zo shi kadai ko kuma tare da wasu abokai ko ‘yan’uwansa; musamman idan ya kasance yana da wata matsala ko takun saka da wani. Ko kuma ya yi basaja ta hanyar zuwa a kamannin wani dan’uwanka ko wanda ka sani don ya hada ka gaba da shi ko gudun ka da ka ramfo shi.