Kowanne miji akwai irin abin da ya fi burge shi a jikin matarsa, yi ƙoƙarin ki dinga kula da abin da zai ja hankalinsa.
Akwai mata masu tallan jikinsu a wajen aiki ko kasuwa da bakin titi. da zarar kin fara haihuwa musamman kirjinki bai da tudu to ki daina zama ba rigar mama. Tsabtace rigunan mamanki akai-akai da fesa musu turare masu kamshi.
- Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata Na Jami’ar Sokoto
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Hana Baƙin Haure Shigowa Nijeriya Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Daga rigunan mamanki sun fara saki, yi maza ki sake sababbi.
Ki dinga sayen (12 ) ko ( 6) kadai ma za su ishe ki.
Sai sun fi dadewa basu saki ba, idan rigar mama ta saki mama ba ya tsayawa cak. Sannan ba’a sa turare a mama, domin maigidanki na sa baki zai ji daci.
ki kiyaye magungunan na bature da wadanda ba su da inganci. Jiki ba a abin wasa bane kada garin gyaran gira a rasa ido. ki gode wa Allah a yadda ya halicce ki duk yadda kike akwai wacce ba ta kai ki ba. Halittarki da kike ta korafi, wata kuma shi take kwadayin samu.
Ki nemi hanyoyin na halal don inganta jikinki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp