Kawo yanzu dai ba batun rudani kan dakatar da Abulrasheed Bawa daga mukaminsa na shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC bisa zarge-zargen cin amanar ofis da aka yi masa.
Wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) ya fitar a daren ranar Larabar da ta gabata, wadda ta bayyana amincewar shugaba Bola Tinubu kan dakatarwar, ta ce an bukaci daraktan ayyuka na EFCC ya karbi ragamar shugabancin hukumar.
Abubuwan da zakuso sani game da mukaddashin shugaban EFCC
Daraktan ayyuka kuma a yanzu mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Abdulkarim Chukkol, ya karbi ragamar shugabancin hukumar nan take.
Chukkol ya karbi mukamin daraktan ayyukan hukumar ne daga hannun Mohammed Abba wanda ya rike mukamin mukaddashin hukumar bayan dakatar da Ibrahim Magu.
Chukkol ya yi Digiri na farko a fannin Kimiyya a Jami’ar Maiduguri, inda ya kammala a shekarar 2000, daga nan kuma ya ci gaba da karatun Difloma a fannin Shari’a a Jami’ar Virginia da ke Amurka a shekarar 2011.
Har ila yau, yana da Diploma kan Tsaron Intanet da Kulawa da bangaren Spectrum.
Ya shiga hukumar EFCC ne a shekarar 2003 kuma ya kai matsayin babban jami’in bincike da daraktan ayyuka.
Chukkol yana wani mataki a makarantar Nazarin Kasa da kasa ta FBI, Quantico.
Tsoffin wuraren da ya rike sun hada da shugaban ofishin shiyya na Fatakwal na EFCC kafin a mayar da shi hedikwatar Abuja.