A daren ranar Litinin din nan ne shugaban kasa, Bola Tinubu, ya nada mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya DIG Kayode Egbetokun, a matsayin mukaddashin babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya gabanin majalisar dattawat a tabbatar da shi.
Har zuwa nadin nasa na baya-bayan nan, Egbetokun an ba shi mukamin Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda kuma mai kula da shiyyar Kudu-maso-Yamma a matsayin mai kula da sashen binciken manyan laifuka (FCID) a hedkwatar rundunar ’Yansanda da ke Abuja tun ranar 6 ga Afrilu, 2023.
- Da Dumi-Duminsa: Tinubu Ya Kori Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Ya Nada Sabbi
- Tinubu Ya Kori Shugabannin Hukumomi Da Ma’aikatu Da Cibiyoyin Gwamnati
An haifi sabon shugaban ’Yansandan ne a ranar 4 ga Satumba, 1964 a Erinja, karamar hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun kuma ya shiga aikin ‘Yansandan Nijeriya a ranar 3 ga Maris, 1990, a matsayin Mataimakin Sufeto na ‘Yansanda na sashen Cadet.
Ya samu horo na farko a makarantar ‘Yansanda ta Nijeriya, kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen rundunar ‘Yansanda.
Ya yi aiki a wasu rundunonin ‘Yansanda da a fadin kasar nan, kuma ya rike mukaman kwamanda a lokuta daban-daban.
A matsayinsa na Mataimakin Sufurtandan ‘Yansanda a shekarar 1999, an nada shi babban jami’in tsaro ga zababben gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, wanda yanzu ya zama shugaban Nijeriya.
Ya yi aiki a matsayin Kwamanda, Rapid Response Squad (RRS), Lagos, Squadron Commander MOPOL da mukamin Anti-Fraud Unit, FCT, Abuja ya kuma zama Babban Sufeton ‘Yansandan gudanarwa na Hedkwatar Rundunar Jihar Legas, Ikeja da kuma Kwamandan shiyya a Osogbo na Rundunar ‘Yansandan jihar Osun kuma kwamandan yanki a Gusau, reshen jihar Zamfara da dai sauransu.
Egbetokun ba jami’in ‘Yansanda ne kadai ba, masanin lissafi ne. Ya kammala karatunsa na farko a Jami’ar Legas, Akoka, inda ya yi digirinsa na farko a fannin lissafi a watan Yuni 1987, sannan ya karantar da ilimin lissafi a Kwalejin Fasaha ta Yaba da ke Legas, kafin ya shiga aikin ‘Yansanda.
Sauran karatuttukansa sun hada da digiri na biyu a sashen nazarin fasaha a Jami’ar Legas, Akoka, 1996, PGD a fannin tattalin arzikin man fetur daga Jami’ar Jihar Delta, Abraka, 2000, da MBA daga Jami’ar Jihar Legas, Ojo a 2004.