Kyaftin ɗin Manchester City, Kyle Walker, ya koma ƙungiyar AC Milan ta Italiya a matsayin aro na tsawon kakar wasa ta bana.
A ranar Alhamis ne ɗan wasan ya kammala gwajin lafiya tare da Milan, ƙungiyar da ta taɓa lashe gasar Zakarun Turai har sau bakwai.
Yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Milan da Walker ta bayar da dama ga Milan ta saye shi idan wa’adin aron ya kare a karshen kakar wasa ta bana.
Walker, wanda ya lashe gasar Firimiya sau shida tare da Manchester City, zai haɗu da ‘yan uwansa na Ingila, Fikayo Tomori da Ruben Loftus-Cheek a San Siro.
Zai sanya riga mai lamba 32 a Milan, kuma ana iya ganin Walker ya fara buga wasa ranar Lahadi idan suka karɓi bakuncin Parma a gasar Serie A.
Walker ya buga wasanni 319 tare da City tun bayan komawarsa daga Tottenham a shekarar 2017 a kan kuɗi fam miliyan 50.