Kungiyar Dattawan Arewa (ACF), ta bukaci sojojin Nijeriya da su sake duba dabarbaru da hikimomin da suke bi wajen magance matsalolin tsaro a arewacin kasar da ma Nijeriya baki daya.
A wata sanarwar da jami’in watsa labarai na kungiyar, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya fitar a ranar Litinin, ACF ta nuna damuwarta kan yadda ake samun ‘yan kura-kurai a aikace-aikacen sojojin.
Kungiyar ta nuna takaici kan yadda jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta a wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Silame a Jihar Sakkwato a ranar Laraba, 25 ga watan Disamban 2024.
Harin wanda ya janyo mutuwar fafaren hula goma da jikkata wasu da dama.
Kungiyar Dattawan Arewan ta yaba wa gwamantin tarayya da gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu bisa hanzarin kai dauki da daukan nauyin jinyar wadanda suka raunata tare da bata wani lokaci ba.
“ACF ta kadu sosai da wannan lamarin na Silame, abun ya yi yawa a kasar nan. Irin wannan harin ya faru a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna da Jihar Adamawa da Nasarawa, da jikkata mutane da dama wanda har yanzu muna fama da wadannan radadin a zukatanmu.”
A cewarsa sanarwar, kungiyar a kowani lokaci tana karfafa gwiwar hukumomin tsaro wajen yaki da kowace nauyin ta’addanci a fadin kasar nan, amma ba hakan ba ne zai ba su damar kashe fafaren hula ba tare da sun ji ko sun gani ba.
“Babu wanda ya isa ya shiga shakku game da irin wannan goyon bayan namu, kuma ACF ta yi kira ga duk wani mai kishin kasa a Nijeriya da ya ba jami’an tsaro goyon baya. Abu ne kawai da ba za a yarda da shi ba a bar ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka na kowane irin launi su rike al’umma don neman kudin fansa ta hanyar ayyukansu na kiyayya.
“Wannan, abubuwan da suka faru irinsu na Silame da sauran wadanda suka faru kafin shi da kuma kididdigar tasirinsu ga ‘yan kasa marasa laifi suna daukar wani tsari mafi tayar da hankali tare da asarar Dan’adam wanda ba za a yarda da shi ba.”
Daga bisani kungiyar ta yi kira ga sojojin da su maida hankali wajen gudanar da ayyukansu bisa kwarewa da sanin ya kamata domin kauce wa faruwar irin wannan lamarin a nan gaba ta hanyar duba dabarun da hikimomin yaki da suke yi wajen kai farmakisu ga ‘yan ta’adda.
Kungiyar Dattawan Arewan ta kuma nemi masu hannu da shuni da kungiyoyi da su kai agaji da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa domin rage musu radadin halin da suke ciki.