• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya

by Alhaji Adamu Rabiu
2 months ago
PDP

“Ungulaye Sun Fara Shawagi”

Yanzu shekarar 2025 ce, kuma saura kusan shekaru biyu kafin zaɓen shekarar 2027 na ƙasa baki ɗaya. Amma ƙungiyar jam’iyyar marasa jagora da ke ƙarƙashin Lemar da ta kece, da ‘yan ƙungiyar kwale-kwale na Fadar Shugaban Ƙasa masu riƙe da wargajenjen Tsintsiya, da kuma tsofaffin masu faɗa a ji, ‘yan ƙungiyar masu tsintar Masara daga jam’iyyar da ba ta da ma haifa, da kuma jam’iyyar ruɗani mai taken ban dariya guda biyu , masu take kamar haka a turance, “Power to the People”- PDP, “Renewed Hope Agenda”- APC, “Justice for All”- ADA, da “Arise & Shine” ko “Arise & Win” – ADC, ba maƙiya ba ne, amma ƙungiyoyin haɗin guiwa ne. Waɗannan su ne ƙungiyoyi marasa amfani da ke neman komawa karagan mulki don ci gaba da shan jinin ‘yan Nijeriya da kuma ƙasar mu Nijeriya da suka riga suka sheƙe ta.

Waɗannan mafarauta su ne ke neman shigowa fagen siyasa da dabarun da ke cikin tsohon littafin ɓarnar su, Kuma ga sunan, sun fara zagaye kamar ungulaye a kan gawar Nijeriya suna jiran su yaudare ku da kuri’unku.

  • Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC 
  • Sai Ƴan Siyasa Sun Haɗa Kansu Sannan Za Su Iya Tunkarar APC A 2027 – Lukman

“Haɗin Gwiwar Mugaye da Makaryata”

Yayin da matasan Nijeriya ke taro a Abuja don daidaita da kuma kammala shawarwarin da aka tattauna a Taron Matasan Ƙasa na 2025, inda na gabatar da shirin ceto Nijeriya mai taken “Taswirar Matasan Nijeriya don Dakatar da Zubar Jinin Dimokuraɗiyya”, wata ƙungiyar barkwanci ta bayyana, wanda jagororanta ba masu kishin ƙasa ba ne, amma masu tsotsan jinin ƙasa ne. Waɗannan mutanen su ne masu riƙe da gadon gazawa da cin hanci da rashawa, ɗau ke da gurɓattacen maganin da suke so Nijeriya ta gurɓa domin ta cigaba da fama da ciwon daji(cancer) ,ciwon da ke kashe ƙasar nan.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Waɗan nan sune suka keɓe makomar Nijeriya, kuma suka yi garkuwa da ita. Har ila yau, a cewar majalisar dattawa ta 9 da ta yi bincike na sayar da ƙaddarorin gwamnati, wanan ɓarnar dukiyar ƙasa ne a rana tsaka, kuma kamar yadda ɗaya daga cikinsu ya bayyana kafin ya koma cikinsu, ya ce: “PRIƁATIZATION” ba komai ba ce face “PIRATIZATION” — wato sata da rabon ganima ce a fili.

Waɗannan su ne masu kuɗi na yaki haram -yaki halas ,da suka ƙwace jam’iyyu, suka wawure zaɓuka, suka yi watsi da kowa sai nasu, suka kashe baitul-mali, kuma yanzu suna neman dawowa bisa kan Karagar Mulki da sunan dimokuraɗiyya. Wannan cutar dimokuraɗiyyar Nijeriya ce da ke ƙara bazuwa, kuma yaudara ne gadan-gadan da rana tsaka!

Ko wanne cikinsu yana da tabon keta doka. Waɗannan ‘yan wasan kwaikwayo ba ‘yan adawa ba ne ga juna, amma abokai ne wajen wawure dukiyar ƙasa da kuma durƙusar da ƙasa marasa kishin Nijeriya ko ‘yan Nijeriya, wanda suke kama da Judasu da ke neman a dawo da shi cikin sahun Manzanni.

“Izaa Zulzilatil Ardu Zilzaalahaa”

“Idan ƙasa ta girgiza da girgizarta ta ƙarshe…” (Suratul Zilzalah, Aya ta 1)

Amma tambaya biyu?:

Lokacin da waɗannan bayi, ‘yan cartel, masu siyar da Nijeriya , suke rike da gwamnati daga 1999 zuwa 2025:

Me suka yi alkawari ga ‘yan Nijeriya?

Me aka tono game da su bisa kundin tsarin mulkin 1999 da dokar sayar da kamfanonin gwamnati (Priɓatization Act), da rahotannin kwamitin majalisa, da ƙasidan el-rufai da bayanan jaridun gaskiya kamar Premium Times, Guardian, Daily Trust, ThisDay, Ɓanguard, Punch, Sahara Reporters da sauransu?

Alƙawura: (Sakamakon ƙarancin wuri, za a kawo kaɗan daga ciki)

Rashin inganci na kamfanonin gwamnati yasa za a sayar da su

Tsauri da wahalar tafiyar da su

Yawan ma’aikata

Rashin riƙon amana

Cin hanci da rashawa

Nauyi ga gwamnati

Rage kashe kuɗi

Samar da ayyukan yi

Shigo da jarin da ƙasashen waje

Gyaran tattalin arziki

Ci gaban ilimi da lafiya

Bunƙasa noma

Yaki da fatara

Samar da tsaro da walwala da dai sauransu…

Amma Abin Da Suka Aikata: Suna da hannu a:

Sayar da Niger Dock, sun kori ma’aikata 3,600

Sayar da Eleme Petrochemicals -Kafanin da ta saye ta tamayar da kuɗin ta har da riban jarin a cikin watani 14 kacal.

ALSCON – An gina ta akan kuɗi dalar amurka $3.2bn, aka sayar da ita akan dalar amurka $130m.

Sayar da Daily Times, NICON Insurance, Transcorp Hilton, da Ughelli Power

NEPA, NITEL, Nigeria Airways, Delta Steel, da sauran su

Cire tallafin man fetur.

Rashin biyan fansho da hakkokin ma’aikata.

Ka da mu manta da labarin akwatuna 53 a fili tashin jirgin saman a legas ( wato the 53 Suitcases Saga).

Da labarin dalar amurka $40m da aka fitar zuwa Amurka.

Takardun makaranta jamiá da shaidar ƙaryar ta Chicago State Uniɓersity.

Raba kan ‘yan Nijeriya da salon tsarin musulim – musulim ticket.

Zargin cin hanci na Grass-cutting a san sanin ‘yan gudun hijira.

Biyan fensho har ƙarshen rayuwa ga manyan sakatarorin gwamnatin taraya (PERM.SECs) da shugaban ma’aikata(Heads of Serɓice) daga asusun IPPIS ba tare da sun bada gudunmawa ba , da dai sauran su.

Rusa tattalin arziki ta karyar da darajan naira.

Ƙarancin abinci da ilimi

Durkusar da noma da kiwo da kuma tsarin noma da ya tsaya cik

Mayar da asibitocin wajen hanyar samun kuɗin shiga da taɓarɓarewan kiwon lafiya.

Rashin tsaro da garkuwa da jama’a da dai sauransu…

Kada mu manta da wanna ayoyin

“Faman ya’mal mithƙaala tharratin khayran yarah”- (Suratul Zilzalah, Aya ta 7)

“Wa man ya’mal mithƙaala tharratin sharran yarah “-(Suratul Zilzalah, Aya ta 8)

“Zaɓin da ke Gaban ‘Yan Nijeriya”

To ga su kamar haka, ‘yan Nijeriya na cewa:

PDP – Power to the People? To ku dawo da duk ƙadarorin da aka siyar ba bisa ƙa’ida ba kuma a siyar da ƙadarorin Dubai domin a kafa cibiyoyin masana’antu na matasa.

APC – Renewed Hope? Ku dawo da tallafin da aka cire, kuma a mayar da gidan Naira biliyan 21 zuwa Asibitin Ƙasa mai daraja ta ɗaya.

ADA – Justice for All? To ku dawo da duk kuɗaɗen da aka wawure daga sayar da ƙadarori da sauran madaƙala da ya faru a ƙarƙashin zamanin ku.

ADC – Arise & Shine? To ku jabaya kuba Nijeriya da ‘yan Nijeriya damar tashi, da haskakawa da cin nasara.

Tsakanin dukkan su dake cikin PDP, APC, ADA da ADC sun more rayuwa, sunyi komai mai yuwuwa a ƙarƙashin sama ta ɗaya, halartatce da haramtatce, ko ƙarya ne?

To kada mu manta da wanna aya -“Fabi ayyi aala’i Rabbikumaa tukazzibaan?”- (Surah Ar-Rahman: Ayoyi 13 da sauran ayoyi 30)

“A Ƙarshe”

Bari mu rufe sharhin da waɗannan kalmomi masu ratsa zuciyar bil adama masu tsoron Ubangiji :

“Inna Allaha ‘ala kulli shai’in shaheed” – Lalle Allah shaida ne a kan komai. (Surah Al-Mujadilah: 6)

“Wallahu khabeerun bima ta’maloon” – Allah yana sane da duk abin da kuke yi. (Surah Al-Hujurat: 18)

“Wa makaroo wa makarallah, wallahu khayrul makireen” – (Surah Al-Imran: 54)

(Su sami malamai su yi masu cikanken bayanin wannan aya)

“Yawma’izinyasdurun naasu ashtaatan liyuraw a’maalahum” – A ranar nan, mutane za su rabu sassa daban-daban domin a nuna musu ayyukansu (munana da kyawawa). (Surah Al-Zalzalah: 6)

Hon. (Alh) Adamu Rabiu (Bakondare)

Ƙwararre a fannin Kula da Ayyuka da Tantance su (M&E) kan Manufofi, Kuɗi, Siyasa da Gudanar da Gwam

nati Mai Kyau, kuma mai fafutukar Ci Gaba Mai Ɗorewa. Ya rubuto daga Kaduna

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027
Siyasa

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu
Siyasa

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson
Manyan Labarai

Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson

October 16, 2025
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 9 A Kogi

Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 9 A Kogi

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.