Wakokin daular Tang
Al’adun daular Tang sun kai matsayin koli na al’adun kasar Sin, musamman ma lokacin samun bunkasuwar wakokin gargajiya zuwa wa’adin samun bunkasuwar daular Tang a duk fannoni. A cikin tarihin daular Tang na tsawon sama da shekaru 300, an samu wakoki sama da dubu 48.9 da suka yadu a lokaci mai zuwa.
A sakamakon haka, an samu fahimtar sunayen marubuta wakoki sama da 2300 bisa wadannan wakokin daular Tang.
A fannin samar da wakokin daular Tang, an dora muhimmanci kan hakikanin abubuwa da ba na gaskiya ba tare. A fannin salolinsu kuma, akwai salo mai jimloli 4 da na jimloli 8, a kowace jimla, akwai kalmomi 5 ko kalmomi 7. Bugu da kari, an samar da wakokin karni na kusa da yanzu masu dadi sosai.
A cikin marubuta wakokin daular Tang, Li Bai da Du Fu sun fi shahara, kuma sun sami suna a duk duniya. A kan kira su biyu “Li-Du”.
An kira Li Bai Waliyin wakoki, wanda yake da kwarewa sosai. Wakokin da ya rubuta cike suke da abubuwan kaga. Sun nuna alfahari ga ni’imtattun wurare na kasar. An samu wakokin Li Bai sama da 990 a yanzu. A cikinsu, wakar “Qiangjinjiu”, da wakar “Shudaonan”, da wakar “Duba magangarar ruwa dake tsaunin Lushan” da dai sauransu, sun shahara kwarai da gaske.
An kira Du Fu Sarkin wakoki. A yayin da yake wani karamin matashi, ya kai ziyara wurare daban daban masu ni’ima. Amma daga bisani, ya gamu da matsaloli da yawa a cikin rayuwarsa. Sai a kai a kai ya samu fahimtar kalubalolin da jama’a su kan gamu da su. A sabili da haka, a cikin wakokinsa, ya kan bayyana wahaloli masu tsanani da jama’a suke sha a cikin zaman rayuwa. An samu wakoki na Du Fu sama da 1400. A ciki, wakoki mafi shahara su ne wakar “Chunwang” da wakar “Tafiyar motocin sojoji”, da wakoki uku dangane da jami’ai (Wakoki uku masu suna “Jami’an Shihao”, da “Jami’an Xin’an”, da “Jami’an Tongguan”), da wakoki uku dangane da yin ban kwana (Wakoki uku masu suna “Yin Ban Kwana da iyali”, da “Yin ban kwana bayan aure ba da dadewa ba”, da “Yin ban kwana da tsoho”) da dai makamantansu.
Bayan haka, shahararrun marubuta wakoki na daular Tang sun hada da Wang Wei, Bai Juyi, Lihe, Li Shangyin, da Du Mu, da dai sauransu.
Ya zuwa yanzu, wakokin daular Tang sun samu karbuwar jama’a kwarai da gaske. Har ma wasu daga cikinsu ko yara suna iya rerawa. Kamar waka mai suna “Yin la’akari a lokacin dare”da Li Bai ya rubuta. A cikin wannan waka, an rubuta yadda ake begyen gari. A cikin wannan waka, an rubuta cewa, an yi ruwan sama a lokacin dare na yanayin bazara. Sannan waka mai suna “Yin farin ciki domin ruwan sama a lokacin dare na yanayin bazara” (Wannan jimla ta zo daga waka mai suna “Hawan husumiyar Guanque” da Wang Zhihuan, marubuci daban ya rubuta) da dai sauransu. A kan yi amfani da wasu shahararrun jimloli dake cikin wakokin daular Tang, kamar “Idan ana neman kara hangen nesa, sai a kara hawan hawa daya na husumiya” (Wannan jimla ta fito daga waka mai suna Qiangjinjiu da Li Bai ya rubuta), da “Ruwan Rawayan Kogi ya zo daga sararin sama” (Takardar rufin maficici dake bayyana abubuwan dake cikin wakokin daular Tang) da dai sauransu. Dadin dadawa, littafi mai suna Wakokin daular Tang guda 300 ya fi samun karbuwar jama’ar Sin da ta ketare a yanzu. A kasar Sin a yau, akwai wani karin magana da cewa, “Idan ana iya karanta wakokin daular Tang guda 300, sai ana iya samar da wakoki”. Ta haka ana iya ganin cewa, Sinawa suna son wakokin daular Tang kwarai da gaske. Ga wasu wakokin daular Tang:
Yin la’akari a lokacin dare
Li Bai
An yi hasken farin wata a gaban gado,
Sai an nuna tababa da cewa ko wannan ne hazo a kasa.
An ta da kai domin duba duniyar wata,
Sai an kada kai tare da begyen gari.
Wakar Jueju
Du Fu
Tsuntsaye iri na Oriole masu launin rawaya guda biyu suna yin murya a kan wani itacen Willow mai launin kore,
Wani ayarin tsuntsayen Egret masu launin fari suna tafiya a sararin sama.
Ana iya ganin kankara dake dutsen Min a yamma ta taga,
A gaban kofa kuma akwai wani jirgin ruwa da zai tashi zuwa kasar Wu ta gabas.
Wakokin daular Song
Wakar Ci, na daya daga cikin salolin wakokin gargajiyar kasar Sin. Akwai sunayenta da dama, shi ya sa ana iya sa mata kide-kide domin rera. Shi ya sa a kan kira ta kidan Ci. Akwai bambanci sosai tsakanin tsawon jimloli. A sakamakon haka, a kan kira ta Wakar jimloli masu tsawo da gajere. Duk wadannan sunaye sun bayyana dangantakar kut-kut dake tsakanin wakar Ci da kide-kide, da kuma hanyar ta daban da wakar Ci take bi. Bayan haka, Ci na da sunayen sauti da dama, wadanda a kan kira su Cipai, kamar “Duniyar wata dake yammacin kogi”, da “Launin ja dake kogi baki daya”, da “Rumengling” da dai sauransu.
A matsayin waka mai sabon salo, wakar Ci ta kai matsayin koli a yayin daular Song. Kamar yadda wakokin daular Tang suke, wakar Song ita ma tana da muhimmanci kwarai da gaske a tarihin adabin kasar Sin.
A lokacin samun ci gaba, an samu marubuta wakar Song masu nuna fifiko da dama, kamar Su Shi, da Li Qingzhao, da Xin Qiji, da Lu You da dai sauransu.
Wakokin Su Shi na da alamar ba kowa masu laushi. Kuma sun shafi fannoni iri daban daban, wasu sun bayyana burinsa na ba da gudummawa ga kasar, wasu sun bayyana abubuwan dake kauyuka, yayin da wasu kuma suka bayyana ra’ayoyin jama’a na bakin ciki.
Li Qingzhao.
Li Qingzhao, shahararriyar marubuciya ce ta daular Song. Wakokinta na da danye, tare da hakikanin tunani. Wasu sun bayyana fahimtarta ga soyayya da burinta a wannan fanni, wasu sun bayyana tasirin da canzawar halittu ta yiwa mutane, yayin da wasu kuma suka bayyana kalubalolin da aka gamu da su a sakamakon lalata kasa da iyalai. Shahararun jimloli da dama sun bayyana kwarewar Li Qingzhao, kamar“Ko ka sani? Kamata ya yi a kara samun ganyaye masu launin kore a maimakon furanni masu launin ja”(Wannan jimla ta zo daga wakar Li Qingzhao mai suna “Rumengling”, wadda ta bayyana abubuwan dake yanayin bazara), da “Ba za a iya kawar da damuwata ba. Da zarar aka kawar da ita daga gira, sai ta shiga cikin zuciya” (Wannan jimla ta zo daga wakar Li Qingzhao mai suna “Yijianmei”, wadda ta bayyana begyenta yadda ya kamata) da dai makamantansu.
Xin Qiji, marubucin daular Song da ya fi samun wakokin Ci. Mafi yawan wakokinsa, cike suke da jaruntaka. Jimloli da dama, kamar “Bayan da na sha giya, na fara wasan takobi, sai na yi mafarki kamar na dawo rundunar soja” (Wannan jimla ta zo daga wakar Xin Qiji mai suna “Pozhenzi”, wadda ta bayyana jaruntakar yaki da sojojin kasar Jin da samun sakamakon mai kyau da bautawar kasar, tare da bayyana ma’anar fushi domin rashin damar cimma burinsa), da “Babban tsauni mai launin kore ba su iya hana tafiyar ruwa ba, wanda ya nufi gabas a karshe.” (Wannan jimla ta zo daga wakar Xin Qiji mai suna “Pusaman”, inda aka waiwaye babbar matsalar da hare-haren da sojojin kasar Jin suka yi suka samar ga jama’ar kasar, tare da bayyana bakin cikinsa na rashin samun damar shiga rundunar soja domin yaki da sojojin kasar Jin) da dai sauransu, ba ma kawai sun bayyana rayuwar sojoji ba, har ma sun bayyana burinsa na yaki da kasar Jin da tunaninsa na son kasa. Wakokinsa da dama sun kara abubuwa da tunani da salolin fasaha da yawa na wakokin Ci na daular Song.
Kawo yanzu dai, wakokin Song Ci na samun karbuwar jama’a kwarai da gaske. Kusan a kowane iyali, ana iya samun littafin “Wakokin Song Ci guda 300”. Dadin dadawa, an tsara sabbin kide-kide ga wasu daga cikinsu domin rera.
Sautin Shuidiao Getou
Yaushe za a iya samun farin wata mai haske? Na tambayi sararin sama tare da giya a hannu. Ba a san lokacin fadar dake sararin sama a yanzu ba. Ina son in tafi zuwa fadar bisa iska. Amma ina jin tsoro da cewa, gine-ginen dake sararin sama na da sanyi sosai. Na yi rawar jiki, kasancewa a yankin bil’adam ya fi komawa fadar dake duniyar wata.
Duniyar wata tana tafiya a ko ina ba tare da yin barci ba. An yi hasken duniyar wata a gaban taga, tare da mutumin dake gado, wanda ba zai iya shiga barci ba. Bai kamata farin wata mai haske ta nuna damuwa sosai ba. Amma ina dalilin da ya sa ba ta yi siffar da’ira ba sai lokacin da aka yi ban kwana. Mutane su kan samu canzawar rayuwa, kamar yin bakin ciki, da yin farin ciki, da yin ban kwana, da yin haduwa, yayin da duniyar wata ta kan yi canzawar siffarta. Ba za a samu sauyawa kan wadannan al’amura ba. Ina fatan kowa zai samu alheri, tare da duba farin wata mai haske sosai, ko akwai nisanta a tsakaninsu.