Saboda sha’awar da suke yi wa kasar Sin, wasu baki ‘yan kasashen waje sun shigo kasar. Domin neman cimma burinsu, wasu har sun zauna a kasar Sin, domin aiki, ko karatu. Mene ne ra’ayin baki ‘yan kasashen waje kan kasar Sin, musamman wadanda ke zaune a nan har na tsawon lokaci?
Kasar Sin da kasar Zambiya na da dadadden zumunci a tsakaninsu. A ranar 29 ga watan Oktoban shekara ta 1964, Zambiya ta kasance kasa ta farko dake yankin kudancin Afirka, wadda ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin, kuma a shekarar da muke ciki wato 2024, aka cika shekaru 60 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. A halin yanzu, Sin da Zambiya na kara yin mu’amala da cudanya da juna ta fannoni daban-daban, har ma zumuncin al’ummunsu na dada inganta.
- Kamfanonin Sin Sun Kara Kirkiro Sabbin Kayayyaki Masu Lambar Kira
- Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Da Su Taimakawa Gwamnatocin Kasashe Masu Fama Da Rikici Wajen Tabbatar Da Rayuwar Yara A Dukkan Fannoni
‘Yan kasar Zambiya da dama sun san kasar Sin daga layin jirgin kasa da aka shimfida tsakanin Tanzaniya da Zambiya, wanda kasar Sin ta taimaka wajen ginawa lokacin da ita ma take fama da talauci. Kawo yanzu kusan rabin karni ya wuce, amma layin jirgin kasan na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen karfafa sada zumunta tsakanin al’ummun Sin da Afirka, musamman na Tanzaniya da Zambiya.
Charlette, daya ce daga cikin ‘yan kasar Zambiya da suka fara sanin labarin kasar Sin daga hanyar jirgin kasa tsakanin kasashen Tanzaniya da Zambiya, wanda ke shaida zumunci mai karfi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Bayan shigowarta kasar Sin zuwa yanzu, Charlette ta kara fahimtar kasar Sin, wadda ke da ci gaban kimiyya da fasaha, da mabambantan wayin kai, da al’umma masu karamci sosai.
“A ganina, mutanen kasar Sin na da kirki da son karbar baki. A nan kasar Sin, ina jin tamkar ina gida Zambiya. Ba na kewar gida sosai, saboda nan tamkar gidana ne.”
Charlette ta sha bayyana cewa kasar Sin tamkar gida yake a wajenta. Kafin ta shigo kasar, tana shakku kan rayuwa da karatu a kasar Sin. Amma iyayenta sun karfafa mata gwiwa gami da ba ta cikakken goyon-baya. A lokacin kuruciyarta, Charlette da mahaifiyarta sun taba ziyartar ‘yan uwansu a Tanzaniya ta hanyar jirgin kasa tsakanin Tanzaniya da Zambiya. Kana, a ‘yan shekarun nan, mahaifin Charlette ya sha zuwa aiki kasar Sin, da ba ta labarin da ya shafi kasar. Har ma mijin babarta dan China, ya ba ta shawarar kara ilimi a kasar Sin. Charlette ta ce:
“Ya ce akwai ci gaban fasahohi sosai a kasar Sin, kuma karatu a kasar zai ba ni karin damarmakin fahimtar al’adun kasar. Shi ma mahaifina ya taba bayyana min labarin ziyararsa a kasar Sin, inda ya ce, ana amfani da wayar salula wajen biyan kudin sayayya a kasar, mutane kadan ne ke amfani da takardun kudi, al’amuran da suka ba ni sha’awa sosai.”
A shekara ta 2019, Charlette ta fara karatu a jami’ar Huaqiao dake birnin Xiamen na lardin Fujian dake kasar Sin. A farkon zuwanta, ta yi iyakacin kokarinta wajen karatun harshen Sinanci, amma tana fuskantar wasu matsaloli, kamar rashin haduwa da iyali da ‘yan uwa da abokai na gida, da rashin gane harshen Sinanci sosai da sauransu. Da take waiwayen farkon zuwanta kasar Sin, Charlette ta ce, ta gode wa malamai da abokan karatunta na kasar Sin sosai, wadanda a cewarta, suka samar mata da cikakken goyon-baya da matukar kulawa, al’amarin da ya taimaka mata sosai wajen haye wahalhalu. Charlette ta ce:
“Na fuskanci kalubale a farkon zuwana kasar Sin. Ni mutumiya ce mai jin kunya, amma malamai da abokan karatuna sun taimake ni sosai, musamman abokan karatuna na kasar Sin. A wani lokaci, na kan yi kuskure yayin da nake magana da Sinanci, amma su kan ba ni hakuri, da koya min yadda zan yi magana daidai. Koyon harshen Sinanci, abu ne mai ban sha’awa, amma kuma mai wahalar gaske. Yanzu zan iya cewa na riga na shawo kan matsalolin.”
A halin yanzu, Charlette tana karatun digiri na farko a tsangayar koyon ilimin injuna masu kwakwalwa dake jami’ar Huaqiao, kuma tana da wani suna na harshen Sinanci, da ake kira Li Yixin. Charlette ta riga ta saba da rayuwa a birnin na Xiamen, inda take jin dadin kyakkyawan yanayin wajen. Charlette ta ce:
“Xiamen, birni ne mai ni’ima da kuma kyan-gani, kuma abincin wurin na da dadi kuma ya dace da ni. Ni ba na son abinci mai yaji. A ganina, Xiamen birni ne mai jan ra’ayin baki ta fannoni daban-daban, farashin kayayyaki na da sauki, haka kuma rayuwa tana da dadi. Ke nan, birni ne mai kyau sosai.”
Charlette ta ce, Sin hamshakiyar kasa ce, kuma tana fatan ziyartar wurare daban-daban a kasar, don ganewa idanunta mabambantan al’adu da yanayin rayuwa a kasar. Charlette ta ce, ban da Xiamen, birni na daban da ya burge ta shi ne Shanghai, inda ta ce:
“Dalilin da ya sa na je Shanghai shi ne, domin abokaina sun ba ni shawarar zuwa sau da dama. Shanghai na da kyan-gani sosai! Na ziyarci husumiyar TV da ake kira Oriental Pearl, da babban ginin Shanghai Tower, wuraren da dama na taba ganinsu a shirin talabijin, amma yanzu na gani a zahiri, kuma gani ya kori ji. Ina matukar farin-ciki.”
Kasar Sin da kasar Zambiya, aminan juna ne masu zumunci sosai a tsakaninsu. Charlette ta ce, kullum ta kan samu labaran mu’amala da hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan zumuncinsu zai kara inganta. Ta ce:
“A karkashin jagorancin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, Sin ta taimaki Zambiya a bangarori daban-daban, ciki har da gina hanyoyin mota, da filayen jiragen sama, da zuba jari a aikin noma da sana’ar kere-kere da sauransu. Duk wadannan ayyukan da kasar Sin ta yi a Zambiya, sun taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasarmu. Kaza lika, na san akwai daliban Zambiya da yawa da a yanzu haka suke kara ilimi a kasar Sin, kuma irin wannan mu’amalar ilimi za ta kara samar da fahimtar juna tsakanin kasashen biyu. Babban abun da nake fatan gani shi ne, Zambiya za ta kara koyon fasahohin zamani daga kasar Sin, musamman a halin yanzu ana sayar da hajojin kasar Sin a duk fadin duniya, ya dace Zambiya ta yi koyi a wannan fanni.”
Asalin Charlette yana Ndola, birni mafi gima na uku a kasar Zambiya, kana birnin da ya shahara sosai a fannin masana’antu. Charlette ta kara da cewa, yin karatu a kasar Sin, zabi ne mafi dacewa da ta yi, ganin yadda kasar take da saurin ci gaba a fannonin tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma, kuma akwai abubuwan da ya kamata kasashen Afirka su koya. Game da burinta a nan gaba, Charlette ta ce, tana fatan za ta koma Zambiya tare da ilimi da fasahohin da ta samu a kasar Sin, don bada gudummawa ga gina kasarta, inda ta ce:
“Ina jin dadin rayuwa a kasar Sin, wani sabon salon rayuwa ne a gare ni. Haka kuma na koyi abubuwa da yawa a nan. Ina fatan zan iya kammala karatu yadda ya kamata a kasar Sin, in koma gida Zambiya tare da ilimi da fasahohin da na koya a nan.”
Kamar ita Charlette, akwai dalibai ‘yan kasashen Afirka da dama, wadanda ke karatu a jami’ar Huaqiao dake birnin Xiamen na lardin Fujian dake kasar Sin, ciki har da Zambiya, Angola, Madagascar, Mauritius, Sudan da sauransu. Kuma har yanzu daliban Afirka da suka gama karatu a jami’ar, suna gudanar da ayyukan da suka shafi kasuwanci tsakanin Sin da Afirka, da mu’amalar al’adu tsakaninsu.
Ilimi, daya ne daga cikin fannonin hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Ban da wannan, kwalliya ta biya kudin sabulu wajen karfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka a sauran wasu fannoni da dama. Alal misali, Sin ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ga Afirka har na tsawon shekaru 15, kana, Sin kasa ce mai tasowa mafi girma da ta zuba wa Afirka jari. Sa’annan a fannin neman zamanantarwa, har kullum kasar Sin ta kan marawa kasashen Afirka baya wajen zamanantar da kansu. A wajen shawarwarin shugabannin Sin da Afirka da aka gudanar a watan Agustan shekara ta 2023, kasar Sin ta bullo da shawarar goya wa Afirka baya wajen raya sana’o’i, da yin alkawarin karfafawa kamfanoninta gwiwa don su baiwa Afirka taimakon raya sana’ar kere-kere, da habaka tattalin arzikinsu ta fannoni daban-daban. Kaza lika, Sin ta yi alkawarin aiwatar da “shirin taimakawa Afirka zamanantar da sana’ar noma”, don kara zuba jari ga sana’ar noma ta Afirka, da fadada hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar kimiyya da fasahar aikin gona, da kokarin kawo sauye-sauye ga sana’ar noma ta Afirka. A dayan bangaren kuma, kasar Sin ta sanar da “shirin hadin-gwiwa na horas da kwararru”, don inganta kwarewar kasashen Afirka ta fuskar raya kansu.
Muna iya ganin cewa, Sin da Afirka za su kara cimma nasarori a hadin-gwiwa da mu’amalarsu a nan gaba, don kara samar da alfanu da alheri ga daukacin al’ummunsu baki daya.