Adadin hada-hadar biyan kudin kasar Sin wato RMB tsakanin kasar Sin da kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” ko kuma BRI a takaice ya karu a shekarar 2021, inda adadin ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 5.42, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 763.4, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 19.6 bisa dari cikin shekara guda, kamar dai yadda wani rahoto na babban bankin kasar ya bayyana.
Babban bankin na Sin, ya ce wannan hada-hada ta kai kaso 14.8 bisa dari, cikin jimillar hada-hadar da kasar Sin ta gudanar da kudin na RMB, tsakanin ta da kasashen ketare a shekarar ta bara.
Kaza lika rahoton ya ce adadin kudaden da aka biya da RMB, a fannin cinikayyar hajoji, sun karu da kaso 14.7 bisa dari, yayin da na jarin kai tsaye da aka zuwa ya kai kaso 43.4 bisa dari.
Rahoton ya kara da cewa, ya zuwa karshen shekarar 2021, kasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyar musayar kudade da kasashe 22, masu nasaba da shawarar ziri daya da hanya daya, ta kuma kafa tsarin biyan kudade da RMB tsakanin ta da karin kasashe 8, dake cikin shawarar ta ziri daya da hanya daya. (Saminu Alhassan)