ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bai Kamata A Maida Iraki Fagen Takarar Siyasa Tsakanin Bangarori Daban Daban Ba

by CMG Hausa
4 years ago
Iraki

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Dai Bing ya bayyana a jiya cewa, yankin da kasar Iraki ke ciki yana da muhimmanci, ganin yadda ke kunshe da kabilu da mabiya addinai da dama, don haka ya kamata a mai da kasar a matsayin mai dinkin yankin da take ciki, a maimakon fagen takarar siyasa tsakanin bangarori daban daban.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a yayin da kwamitin sulhun MDD yake bincike kan batun kasar Iraki, inda ya ce kasar Sin ta yaba wa Iraki bisa kokarin ta na sada zumunta, da sa kaimi ga hadin gwiwa a yankin da take ciki, kana ta nuna goyon bayan matakin kasashen Iraki da Kuwait, a aikin da suke yi na kokarin gano wasu ‘yan kasar Kuwait da suka bace, da maido da dukiyoyin kasar Kuwait.

  • Wakilin Sin Ya Kalubalanci Amurka Da Ta Daidaita Matsalar Nuna Bambancin Launin Fata A Ayyukan ’Yan Sanda Da Sauransu

Ya ce Sin tana tsayawa tsayin daka, kan manufar kiyaye ikon mulkin kai, da cikakkun yankunan kasa ciki har da na kasar Iraki, tana kuma son ganin yadda ake kiyaye tsaro ta hanyar hadin gwiwa.

ADVERTISEMENT

Dai Bing ya kara da cewa, a halin yanzu, kasar Iraki tana cikin lokaci mai muhimmanci a fannin siyasa, wanda cikin sa ake fuskantar manyan ayyuka, kamar kafa sabuwar gwamnati.

Don haka kasar Sin ke fatan bangarori daban daban na kasar Iraki, za su kara hadin gwiwa, da daidaita matsalolinsu, da cimma daidaito kan harkokin siyasa, ta hanyar yin shawarwari bisa kundin tsarin mulki da dokokin kasar, ta yadda za a kai ga aza tubalin siyasa, a kokarin samun zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa da wadata a kasar.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Ya ce ya kamata sassan kasa da kasa su girmama ikon mallakar yankunan kasar Iraki, su nuna goyon baya ga jama’ar kasar wajen zaben hanyoyin bunkasa kasarsu masu dacewa da yanayin ta. (Zainab)

Iraki
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
SANARWA: A Shirinmu Na Twitter Space Na Yammacin Yau…

SANARWA: A Shirinmu Na Twitter Space Na Yammacin Yau...

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.