Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce a shekarar nan ta 2024, adadin hatsi da kasar Sin ta samu daga noma ya kai tan miliyan 706.5, adadin da ya karu da kaso 1.6 bisa dari kan na shekarar bara, kamar dai yadda wasu alkaluman hukumar suka tabbatar.
NBS ta ce a bana, a karon farko, kasar Sin ta kai ga cimma nasarar samun yawan hatsi da ya haura tan miliyan 700. Kafin hakan, cikin shekaru 9 a jere, kasar Sin na samun adadin hatsi da ya haura tan miliyan 650 a duk shekara. (Saminu Alhassan)